Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 19:44:08    
Wani mutumin kasar Sin na zamanin da mai suna Hai Rui

cri

Hai Rui shi ne wani jami'in daular Ming na karni na 16 na wani wurin kasar Sin. A duk rayuwarsa, ya fid da tsoron kome ba tare da koda kansa ba, ya nuna tausayi ga jama'a da kuma yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka aikata miyagun laifufuka da kuma nuna goyon baya ga jama'a, an yada ayyukan bajinta da ya yi a tsakanin jama'ar kasar Sin.

An haifi Hai Rui a wani gidan jami'an kasa, daga cikin mutanen iyalinsa, wadanda suka sami mukaman gwamnatin wurare na da yawa. Amma a lokacin da yake karami, gidansa ya kan fama da talauci, a lokacin da ya cika shekaru hudu da haihuwa, mahaifinsa ya mutu, ya yi zaman rayuwa tare da mahaifiyarsa kawai. Wajen mahaifiyarsa, jan zuciya gare ta, kuma ta kula da harkokin gidansu sosai cikin tsimi , ta kware wajen horar da 'ya'yanta, ta ciyar da mutanen iyalinta ta hanyar yi wa sauran mutane dinki . Ta mai da hankali sosai ga ba da ilmi ga Hai Rui, a karkashin idon da ta sa gare shi, Hai Rui ya sami tarbiyya sosai tun lokacin da ya ke karami.

Bayan da Hai Rui ya balaga, ya dau wani mukanin sa ido ga ayyukan wuri wuri cikin dogon lokaci, wuraren da ya dauki nauyi bisa wuyansa wajen kula da harkokinsu sun hada da birnin Nanjing da Suzhou da Changchou da sauransu, wadannan wurare su ne wurare masu wadata sosai a da, amma bayan da Hai Rui ya sa kafarsa a wurin, sai ya gano cewa, jama'ar wurin sun yi fama da talauci sosai bisa sanadiyar wulakancin da jami'ai masu cin hanci da rashawa suka yi musu tare da haraji mai tsanani da aka buga musu. Idan a cikin shekarar da ke haifar da bala'In ambaliyar ruwa, to farashin hatsi ya yi hauhawa sosai da sosai, jama'ar farar hula da yawa sun yi gudun hijira zuwa sauran wurare . Bayan da Hai Rui ya hau kujerar mukaminsa, sai ya gyara inda aka lalata bisa sanadiyar ambaliyar ruwa, a sa'I daya kuma ya yi ayyukan ba da agaji, kuma ya yi ayyuka da yawa domin daidaita matsalar yanzu da ta nan gaba.

Don daidaita matsalar fama da talauci a tsakanin manoma, Hai Rui ya yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka aikata miyagun ayyuka, ya nemi masarautan kasa da su mayar wa manoma gonakin da suka kwace daga hannunsu . A wurin, da akwai wani jami'in da ya riga ya yi ritaya, sunansa shi ne Xu Jie, ya taba ba da taimako ga Hairu. Gonakin da ya mamaye na da yawan gaske, amma gonakin da ya mayar wa manoma kadan ne, sai Hai Rui ya rubuta masa wasika don shawo kansa wajen mayar da gonaki da yawa, amma Xu Jie ya ki, a karshe dai Hai Rui ya yi hadin guiwa da sauran jami'ai don aika sako ga sarki, sai Xu Jie ya ga tilashi ne ya mayar da rabin gonakin da ya mamaye .sa'anan kuma Hai Rui ya yanke hukunci mai tsanani ga 'ya'ya biyu na Xu Jie bisa dokokin shari'a, sauran masarautan kasa sun ga ayyukan da Hai Rui ya yi wa Xu Jie, sai nan da nan suka mayar wa manoma gonakin da suka mamaye .

Wajen buga haraji, Hai Rui ya kuma rage nauyin da ke bisa wuyan jama'a. A wancan zamani, wasu masarautan kasa ba su biya haraji ko biya haraji kadan, amma manoman da suke da gonaki kadan su ne suke biyan haraji da yawa, a gaskiya dai , nauyin da ke bisa wuyan manoma ya kara tsanani bisa sanadiyar rashin biyan haraji da masarautan kasa suka yi, sai Hai Rui ya shirya mutane don yin bincike kan gonaki da kuma saukaka tsarin buga haraji don rage nauyin da ke bisa wuyan jama'a.

Ayyukan da Hai Rui ya yi ya kawo cikas ga moriyar masu sukuni, sai suka rubuta wasika ga sarki don shafa masa kashin kaza, sarkin da bai san hakikani abu ba ya kore shi daga mukaminsa. Daga nan Hai Rui ya yi zaman rayuwa kawai a garinsa cikin shekaru 16, har zuwa ranar da ya mutu.

Bayan da ya mutu, yawan dukiyoyinsa da ya bari ba su kai na jama'ar farar hula ba, a duk rayuwarsa, ya ki cin hanci da rashawa, ya sami kauna daga wajen jama'a duban jama'a, wajen jama'ar kasar Sin, Hai Rui shi ne alamar adalci gare su, a wurare daban daban, har zuwa yanzu, ana yin wasannin kawikwayo dangane da shi.(Halima)