Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 18:19:10    
Masana masu ilmin noma na kasar Sin sun taimake mu wajen samar da abinci lami lafiya, in ji minitan noma na Nijeriya

cri
Kasar Nijeriya wata kasa ce mai muhimmanci a fannin aikin noma a yammacin kasashen Afirka. A cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta aika da masana masu fasahar aikin noma da yawa zuwa kasar Nijeriya, bisa tsarin yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Sun shiga kauyukan wurin, inda suka ba da jagoranci kan aikin noma a fuskar fasaha, yin hakan ya kyautata fasahar aikin noma da kuma zaman rayuwar kauyawa na wurin sosai. A lokacin da yake zantawa da wakilinmu Bello da ke Lagos a kwanan baya, ministan harkokin aikin noma na kasar Nijeriya Bamidele Dada ya darajanta ayyukan da masana masu ilmin aikin noma na kasar Sin suke yi, ya kuma nuna fatan alheri kan kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasarsa da kasar Sin wajen aikin noma.

A yankin yammacin kasashen Afirka, har kullun batun samar da abinci lami lafiya yana matsa wa mutane lamba. Saboda a kan samu bala'i daga indallahi na fari da farin dango kullun, shi ya sa kasashe na wannan yanki su kan fuskanci karancin abinci a lokaci-lokaci. A matsayin muhimmiyar kasa wajen samar da abinci a wannan yanki, bunkasuwar aikin noma ta kasar Nijeriya tana da muhimmanci sosai wajen tabbatar da samar da abinci cikin kwanciyar hankali a yankin. Ministan harkokin aikin noma na kasar Nijeriya Mr. Dada ya bayyana cewa, yanzu gwamnatin kasar yana aiwatar da shirin musamman kan samar da abinci lami lafiya a kasar. Ya ce,'Ko da yake kasar Sin tana da mutane da yawa, amma ta biya bukatar abinci a gida, sa'an nan kuma ta fitar da abinci zuwa kasashen waje. Kasar Nijeriya tana son tabbatar da samar da abinci lami lafiya a gida, haka kuma, ta sayar da abinci zuwa ga sauran kasashen Afirka, don taimake su wajen samar da abinci cikin kwanciyar hankali, kamar yadda kasar Sin take yi, '

Mr. Dada ya kara da cewa, a lokacin da take aiwatar da wannan shiri, kasar Nijeriya ta sami babban taimako daga kasar Sin. Masana masu ilmin aikin noma na kasar Sin kimanin 500 sun taba zuwa Nijeriya sun zama mashawarta a fannin fasahar noma a cikin shekarun nan da suka shige. Ya kuma yi bayani kan ayyukan da wadannan masana suka yi, ya ce,'Wadannan masana sun shiga kauyuka, sun yi zama tare da kauyawa, su koyar da su da fasahar noma. Saboda aiwatar da wannan shirin hadin gwiwa, masanan kasar Sin sun ba da taimako wajen kafa kananan madatsan ruwa 14, da rijiyoyi 92 da kuma wuraren tattara ruwa 3. Ayyukan da suka yi sun taimaki mutanen wurin wajen warware matsalar karancin ruwan sha da kuma ruwan da aka yi amfani da shi wajen ban ruwa. Bugu da kari kuma, masanan kasar Sin sun yi tallafawa a fannoni da yawa. Masanan kasar Sin sun taka babbar rawa wajen taimakon kasar Nijeriya don aiwatar da shirin musamman kan samar da abinci lami lafiya.'

Ban da wannan kuma, masanan kasar Sin suna da fasahohi na zamani a fannin yin gyare-gyare kan aikin noma zuwa na zamani da kasar Nijeriya take yi a yanzu. Mr. Dada ya ce,'Wasu masanan kasar Sin suna gina manyan sansanonin samar da abinci da kuma cibiyar samar da amfanin ruwa a jihar Kebbi.'

Ya kuma nuna cewa, yanzu kasar Nijeriya tana neman kara yawan shirye-shiryen bunkasuwa, ta haka manoma za su kara koyon sakamako mai nagarta da fasaha daga hannun masanan kasar Sin. Ya ce,'Yanzu ana aiwatar da shirye-shirye 109. Mun raba ko wace jihar kasar zuwa yankuna 3, ko wane yanki yana aiwatar da wani shiri. Shi ya sa jimlar shirye-shiryen da ake aiwatarwa ta kai 109. Yanzu muna tattara kudi don kara yawan shirye-shirye da sau 3, wato zuwa guda 327. A sakamakon haka, wurare da yawa za su aiwatar da irin wadannan shirye-shirye, kuma manoma za su kara koyon sakamako mai nagarta da fasaha daga hannun masanan kasar Sin.'(Tasallah)