Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 14:21:26    
Mutane masu karancin basira suna jin dadin wasannin motsa jiki

cri

Daga ran 15 zuwa ran 20 ga wata,an yi gasar da aka shirya bisa gayyata ta duniya ta Shanghai ta taron wasannin Olimpic na musamman na shekara ta 2006 a birnin shanghai dake kudancin kasar Sin,an shirya taron wasannin Olimpic na musamman ne musamman domin mutane masu karancin basira.A gun gasar da aka yi,`yan wasa na wasannin Olimpic na musamman da suka zo daga wurare daban daban na duk fadin duniya sun ji dadin wasannin motsa jiki sosai.

A gun gasar,gaba daya an gayyaci `yan wasa da malaman wasa fiye da 2000 daga kasashe da shiyyoyi sama da 20,kuma gasannin da aka yi sun kumshe da wasanni 30,alal misali wasan tseren gudu da takalma masu taya da wasan kwallon kwando da wasan daukan nauyi da wasan iyo da wasan kwallo mai laushi da wasan kwallon badminton da sauransu.Kwamitin shirya gasannin ya bayar da lambar yabo ta zinari da azurfa da kuma tagulla ga `yan wasan da suka sami lambawan da lambatu da kuma lambatiri,ban da wannan kuma,ya bayar da dogon zanen yabo ga wadanda suka sami lamba ta hudu zuwa takwas.

Wasan tseren gudu da takalma masu taya shi ne irin wani wasa mai wuya,amma bayan atisaye mai tarin yawa da aka yi,`yan wasa masu karancin basira su ma suna iya wasan sosai.An shirya gasar wannan wasa a dakin wasan tseren gudu da takalma masu taya na Huangpu na Shanghai,`yan kallo sun ji mamaki kwarai ga fasahar da suka nuna.Malamin wasa na kungiyar kasar Sin Yu Jianbing ya yi mana bayani cewa,ya kasance da hadari yayin da ake yin wannan wasa,dole ne `yan wasa su yi hankali wajen kare jikinsu,`yan wasa masu karancin basira su ma suna iya wasan sosai bayan kokarin da suka yi,kuma za su ji dadi kamar sauran mutane.Malamin wasa na kungiyar wakilan kasar Sin Xue Mu ya ce,`Lallai `yan wasa masu karancin basira suna jin dadi,kuma suna jin alfahari sosai saboda suka sami iznin shiga gasa a madadin mutanen kasar Sin.`

A gun gasar,kungiyar `yan wasa ta kasar Poland ta zama zakara ta gasa ta gudun ba da sanda mai tsawon mita 200 tsakanin mace da namiji,malamin wasan kungiyar Jan Waliskowski ya ce,  `Muna jin farin ciki kwarai da gaske saboda mun sami iznin zuwa nan kasar Sin domin shiga gasanni,yau ma mun ci nasara,muna fatan za mu ci gaba da cin nasara nan gaba.`

Malamin wasa Xue Mu ya yi mana bayani cewa,`yan wasa masu karancin basira sun shiga taron wasannin Olimpic na musamman,ko shakka babu sun ji dadi,ban da wannan kuma,wasannin motsa jiki zai taimake su wajen kyautata zaman rayuwarsu na yau da kullum,ana iya cewa,wasannin motsa jiki suna da amfanin musamman ga wadannan mutane.

Don gudanar da taron wasannin Olimpic na musamman lami lafiya,kwamitin shirya taron ya gabatar da aikin hidima mai kyau,kuma samarin ba da hidima bisa sa kai na Shanghai sun sanya iyakacin kokari,a karshe dai,an samu cikakkiyar nasara.

A shekara ta 2007 wato shekara mai zuwa,za a shirya zama na 12 na taron wasannin Olimpic na musamman na yanayin zafi na duniya a birnin shanghai,ana iya cewa,gasar nan da aka shirya bisa gayyata a Shanghai ita ce gasar share fage da aka yi domin babbar gasa ta shekara mai zuwa.A gun gasar,birnin shanghai ya samar da aikin hidima mai kyau ga `yan wasa na kungiyoyin wakilan kasashe daban daban,`yan wasa da malaman wasa da aka gayyata sun ji dadin nishadi da annashuwa a Shanghai sosai.

Mataimakin firayin ministan kasar Sin Hui Liangyu ya hallarci wasu ayyukan da abin ya shafa da aka shirya a gun gasar,ya bayyana cewa, `Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan taron wasannin Olimpic na musamman da sha`anin kula da nakasassu,kuma ana mayar da wannan aiki a matsayin abu mai muhimmanci wajen tabbatar da zaman jituwa a kasar Sin.Tun daga shekara ta 1987,bi da bi ne kasar Sin ta shirya taron wasannin Olimpic na musamman a duk fadin kasa sau hudu,wannan ya ba da babbar gudumuwa wajen aikin ba da taimako ga mutane masu karancin basira,yanzu dai gwamnatin kasar Sin tana kara ba da muhimmanci kan wannan aiki,haka kuma za a ciyar da sha`anin kula da nakasassu gaba bisa babban mataki.` (Jamila Zhou)