Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 14:19:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(19/10-25/10)

cri
Ran 22 ga wata,an bude zama na 5 na dandalin wasannin motsa jiki da ba da ilmi da kuma al`adu na duniya wanda za a shafe kwanaki 3 ana yinsa a birnin Beijing,an shirya wannan dandali ne a karkashin jagorancin hukumar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al`adu ta majalisar dinkin duniya da kwamitin wasannin Olimpic na duniya,kuma a kan shirya dandalin sau daya a duk shekaru biyu,babban batunsa shi ne don tattauna kan huldar dake tsakanin wasannin motsa jiki da zaman lafiya da huldar dake tsakanin ba da ilmin Olimpic da al`adu.Wannan karo na farko ne da kasar Sin ta shirya dandalin,gwanaye da masana da jami`an gwamnatoci da mutanen da abin ya shafa fiye da 650 da suka zo daga kasashe da shiyoyyi sama da 150 sun hallarci wannan dandali.

Ran 22 ga wata,an yi gudun ba da wutar yula ta zama na 15 na taron wasannin Asiya na Doha a birnin Beijing,an fara aikin ne daga filin Tian`anmen,yarima na kasar Quatar Al-Thani ya sa wuta kan yula,kuma ya mika wa magajin birnin Beijing Wang Qishan yular,daga baya kuma an fara gudun ba da wutar yula.Tsawon gudun a Beijing zai kai kilomita 26.8,gaba daya mutane 89 sun shiga aikin.Daga ran 1 zuwa ran 15 ga watan Disamba na wannan shekara,za a yi taron wasannin Asiya a birnin Doha na kasar Quatar.

Ran 21 ga wata,an rufe zama na 39 na gasar cin kofin duniya na wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe a birnin Aarhus na kasar Denmark,a gun gasannin da aka yi a wannan rana,`dan wasa daga kasar Sin Yang Wei ya zama zakaran gasar parallel bars ta maza,`yar wasa daga kasar Sin Cheng Fei ta sami lambawan na gasar wasannin motsa jiki a kan dandali na mata,gaba daya kungiyar `yan wasan kasar Sin ta sami lambobin zinari guda 8 daga cikin 14.

Ran 22 ga wata,an yi babbar gasa ta karo na karshe ta gasar cin kofin duniya ta wasan harba kibiya ta shekara ta 2006 a birnin Mayapan na kasar Mexico,hadaddiyar kungiyar wasan harba kibiya ta duniya ce ta shirya wannan gasa,`yar wasa daga kasar Sin Zhang Juanjuan ta zama zakara,`yar wasa daga kasar Sin Qian Jialing ta sami lambatu.

Ran 21 ga wata,kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta sanar da cewa,`dan kasar Servia Dujkovic ya zama babban malamin wasa na kungiyar samari ta wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin,zai hallarci taron wasannin Olimpic na Beijing na shekara ta 2008 tare da kungiyarsa.(Jamila zhou)