Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-24 17:23:20    
Yaran da suka sha nonon iyaye mata sun fi lafiya

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, yaran da suka sha nonon iyayensu mata sun fi lafiya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: kasar Sin tana yin kokari domin rage yawan mata masu ciki da suke mutuwa a yankuna masu fama da talauci na Sin. To, yanzu ga bayanin.

A cikin kwanakin nan da suka gabata, kwararru na kasar Rasha sun gano cewa, yaran da suka sha nonon iyayensu mata sun fi lafiya tun lokacin haihuwarsu har zuwa lokacin kuruciya idan an kwatanta su da yaran da ba su sha nonon iyayensu ba.

Kowa ya sani, shan nonon iyaye mata zai ba da taimako sosai ga yara, amma yanzu mata na kasar Rasha kadan daga cikinsu ne suka iya tsayawa kan shayar da yara nononsu. Kwararrun cibiyar binciken ilmin likita ta Kirov ta kasar Rasha sun yi wa yara 1238 bincike, kuma sun raba su cikin kungiyoyi biyu, daya shi ne kungiyar shayar da yara nonon iyayensu mata, yaran da suka sha nonon iyayensu mata fiye da watanni tara sun shiga kungiyar. Dayan kuwa shi ne kungiyar da ba a shayar da yara nonon iyayensu mata ba, yaran da ba su sha nonon iyayensu mata ba da kuma wadanda lokacin da aka shayar da su nonon iyaye bai kai watanni uku ba sun shiga kungiyar.

Kwararru sun mayar da karfin garkuwar jiki da ya zama ma'aunin lafiyar yara. Daga baya kuma sun gano cewa, kungiyar yara da aka shayar da nonon iyayensu mata ta nuna fiffiko a bayyane a lokacin haihuwarsu. A cikin shekara guda da aka haife su, yawan yaran da suka sha nonon iyayensu mata wadanda suka kamu da ciwon hanyar numfashi ya kai rabi idan an kwatanta shi da na daga kungiyar daban. Amma kusan rabin yaran da ke cikin kungiyar da ba a shayar da su nonon iyayensu mata ba sun kamu da ciwon hanyar numfashi har sau hudu a cikin shekara guda bayan haihuwarsu, kuma jariran da yawansu ya kai kashi 6 cikin dari sun kamu da ciwon huhu.

Bugu da kari kuma a lokacin kuruciya, yaran da ba su sha nonon iyayensu mata ba ba su da lafiyar jiki idan an kwatanta su da wadanda suka sha nonon iyaye mata. Yaran nan sun fi saukin kamuwa da ciwace-ciwacen hanyar numfashi da ciwon ciki.