Dutse na Wuquan yana arewacin tsaunukan Gaolan, tsayinsa ya kai mita 1,600 daga leburin teku. Ma'anar sunan wannan dutse a Sinance ita ce, dutse tare da idanun ruwa guda 5. A gaskiya ne kuma akwai idanun ruwa 5 masu dogon tarihi a kansa, su ne idanun ruwa na Meng da Hui da Sweet Dew da Mozi da kuma Juyue. Idon ruwa na Meng yana gabashin wannan dutse, idon ruwa na Hui a yamma. Akwai wata alamarar cewa, a zamanin daular Xihan na kasar Sin, wato tun daga shekarar 206 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa shekarar 23 bayan haihuwar Annabi Isa, wani sharaharren dan baiwa mai ilmin aikin soja saurayi sunansa Huo Qubing ya gwanance wajen harba baka da kuma hawan doki sosai, ya taba shugabantar sojojinsa yada zango a dutse na Wuquan don ci gaba da yawon ganin kwaf zuwa yamma a shekarar 120 kafin haihuwar Annabi Isa.
Huo Qubing ya fara ransa na aikin soja a lokacin da shekarunsa ya kai 17, ya taba yawon ganin kwaf a karkashin shugabancin kawunsa Wei Qing sau da dama don yaki da 'yan Hun mahara. Wei Qing shi ma wani shahararren kwamanda ne da ya kai hare-hare sau 7 ga 'yan Hun daya bayan daya don gudun barazanar da 'yan Hun suka kawo a farkon zamanin daular Xihan. An nada Huo Qubing kwamanda a lokacin da yake da 19 da haihuwa, ya kuma shugabanci sojojin gwamnatin daular Xihan yaki da 'yan Hun. Huo Qubing ya kawo wa 'yan Hun babbar hasara. Sarki Wudi na daular Xihan ya nemi gina wani babban gida ga Huo Qubing domin babbar gudummawarsa, amma Huo ya ki karba, ya ce, bai kori dukan 'yan Hun mahara ba tukuna, ko zai iya zama a cikin babban gida? Amma abin bakin ciki shi ne Huo Qubing ya rasu a lokacin da yake da 23 da haihuwa kawai.
Har zuwa yanzu wasu dadaddun gidajen ibada suna ci gaba da kasancewa a kan wannan dutse, wadanda aka gina su a zamanin daular Ming da Qing. An mayar da dutsen nan tamkar wurin shakatawa ga mutane tun daga shekarar 1995.
Bayan da suka yi dogon lokaci suna hawan dutse na Wuquan, mutane sun sami babban yabo, su iya hangen birnin Lanzhou duka.
|