Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-24 16:44:32    
Dangantakar da ke tsakanin Sin da Massar tana kara samun bunkasuwa

cri

Hadin kan kasashen Sin da Massar a fannin al'adu yana kara samun bunkasuwa cikin sauri. A shekarar 2002 da ta 2004, bi da bi ne kasashen Sin da Massar sun shirya makonnin al'adu a kasashen biyu. A halin yanzu dai, jami'ar Kairo ta kasar Massar tana shirya kafa cibiyar Confucious ta farko a yankunan Larabawa, ta yadda za a kebe wani sabon fili domin bayyana al'adun kasar Sin. To, duk wadannan abubuwa da muka ambata sun taka wata muhimmiyar rawa wajen kara sanin juna a tsakanin jama'ar Sin da Massar.

Shekarar 2006 da ta cika shekaru 50 da kasashen Sin da Massar suka kafa dangantakar diplomasiyya, ta zama wata muhimmiyar alama ce ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Massar da ta Sin da kasashen Larabawa da kuma Sin da kasashen Afirka. A nan gaba, tabbas ne za su kara zurfafa dangantakar abokantaka da ke tsakaninsu bisa tushen amincewar juna a fannin siyasa da samun bunkasuwa tare a fannin tattalin arizki da kuma yin mu'amala da koyon juna a fannin al'adu, kuma za su kara sa kaimi ga hadin kai irin na aminci a tsakanin Sin da kasashen Larabawa da Sin da Afirka, kuma za su kara ba da taimako ga samun bunkasuwar duniya mai jituwa.(Danladi)


1  2