Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-24 16:30:54    
Mr Tang Jiaxuan ya bayyana muhimmancin taron koli na Beijing na dandalin tataunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika

cri

A ran 23 ga wata, wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya kai ziyara ga Mr Tang Jiaxuan, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin don jin ta bakinsa, dangane da hulda a tsakanin Sin da Afrika, da muhimmancin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin guiwar tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Wakilin kamfanin Xinhua ya yi wa Mr Tang Jiaxuan tambaya cewa, ina ra'ayinka a kan ci gaba da aka samu wajen yalwata hulda a tsakanin Sin da Afrika, da kuma halin da ake ciki dangane da huldar?

Mr Tang Jiaxuan ya amsa cewa, ko da yake ya kasance da nisa sosai a tsakanin Sin da nahiyar Afrika, amma duk da haka tun fil azal ya kasance da dangantakar aminci a tsakaninsu. Kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949 ya bude wani sabon shafi ga huldar da ke tsakaninsu. A watan Mayu na shekarar 1956, an kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Masar, nan ta ke an shiga wani sabon lokaci don bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ya zuwa yanzu, yawan kasashe da suka kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu da kasar Sin ya kai 48.

A cikin shekaru 50 da suka wuce, jama'ar Sin da ta kasashen Afrika sun raba fara daya, sun nuna wa juna juyayi da goyon baya. Ko da yaushe kasar Sin tana nuna goyon bayanta ga kasashen Afrika bisa kokarin da suke yi wajen kare mallakar kansu da 'yancin kansu da kuma bunkasa tattalin arzikinsu, ta ba da taimakonta wajen kare zaman karko a Afrika a fannin siyasa da raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

A sa'i daya kuma, kasashen Afrika su ma sun nuna wa kasar Sin babban goyon baya mai daraja. Aminamu na Afrika sun ba da tabban taimako wajen maido wa Jamhuriyar Jama'ar Sin halaliyar kujerarta a majalisar dinkin duniya, kuma ta nuna wa kasar Sin babban goyon baya wajen yin watsi da shirin bututuwa da kasashen yammaci suka gabatar na yin adawa da kasar Sin a gun taron hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya. Yawancin kasashen Afrika suna tsayawa tsayin daka wajan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da nuna goyon baya ga babban sha'anin dinkuwar kasar Sin gu daya, kuma sun sha bai wa kasar Sin taimako wajen murkushe makarkashiya da Taiwan ta kulla don neman shiga cikin majalisar dinkin duniya da hukumar kiwon lafiya ta duniya. Ka zalika kasar Sin ta sami taimako daga wajen aminanmu na Afrika wajen neman samun damar shirya wasannin Olympic na shekarar 2008 da babban bikin baje-koli na duniya na shekarar 2010 tare da nasara.

Wakilin kamfanin Xinhua ya kara tambaya cewa, wadanne irin matakai da kasar Sin za ta gabatar don yalwata huldar da ke tsakaninta da kasashen Afrika?

Mr Tang Jiaxuan ya amsa cewa, a shekarar 2000, bangarorin Sin da Afrika su ne suka gabatar da shawara ga yin taron dandalin tattaunawa a kan hadin guiwarsu. Babban jigon taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da za a yi a wannan gami, shi ne "aminci , zaman lafiya, hadin kai, da bunkasuwa ". Bisa wannan babban jigo, Shugabannin Sin da na kasashen Afrika za su waiwayi sakamako da aka samu, tun bayan da Sin da kasashen Afrika suka fara dankon aminci da hadin kai a cikin shekaru 50 da suka wuce, kuma suka fara yin taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakaninsu a cikin shekaru 6 da suka gabata. Haka kuma za su amince da yalwata sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afrika bisa manyan tsare-tsare, su tsara fasalin hadin guiwar da bangarorin biyu za su yi nan gaba, su yi musanyar ra'ayoyinsu a kan manyan batutuwan duniya da na yankuna.

A lokacin taron, bangaren Sin zai gabatar da ra'ayoyi da shawarwari da yawa a kan inganta dangantakar da ke tsakaninta da Afrika. Kuma zai gabatar da hakikanan matakai da za a dauka don ba da taimako wajen gaggauta raya kasashen Afrika, ta yadda za a aiwatar da matakai guda biyar da kasar Sin ta bayyana wajen ba da taimako ga raya kasashe masu tasowa.

Mr Tang Jiaxuan ya hakake, taron zai zama wani sabon al'amari ga tarihin sada zumunta a tsakanin Sin da Afrika. (Halilu)