Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-23 19:56:11    
Kasashen Afrika suna kara samun zaman lafiya da bunkasuwa

cri
Jama'a masu karantawa, a cikin labarun da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka bayar, da akwai wasu da suka shafi babbar nahiyar Afrika, a cikinsu ana kan samun labaru dangane da talauci da hargitsi da koma baya. Amma hakikanan abubuwan ba hakan ba ne. Kwanan baya, wata direktar ofishin binciken al'amuran Afrika na cibiyar binciken yammacin Asiya da Afrika ta mahadar kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin mai suna He Wenping ta karbi ziyarar da manema labaru na gidan rediyon kasar Sin suka yi mata, inda ta bayyana wa wakilanmu wata Afrika da ke da bambanci da wadda kafofin kasashen yamma suka fahimta ta, wato Afrikar da ke kara samun zaman lafiya da bunkasuwa.

Babbar nahiyar Afrika wadda mai kafa tushen hasashen binciken sauyawar halittu Charles Robert Darwin ya tabbatar  mata da cewar wai wuri ne mafarin 'yan Adam. Tun daga zamanin aru aru, tana da wayewar kai mai haske sosai, amma a zamanin yau, in an kwatanta ta da sauran nahiyoyin duniya, ana iya ganin cewa, tana koma baya wajen samun bunkasuwa bisa sanadiyar mulkin mallaka da aka yi cikin dogon lokaci da hargitsin da ake ta yi. Amma, a ganin malama He Wenping , irin halin da kasashen Afrika suke ciki a cikin tsakiyar shekaru 90 na karnin da ya shige ya riga ya sami manyan sauye-sauye, ta bayyana cewa, tun daga tsakiyar shekaru 90 na karnin da ya shige har zuwa yanzu , ana iya ganin cewa, bisa albarkacin kara aiwatar da dimokuradiya a kasashen Afrika, sai hargitsin da aka yi cikin kasashen Afrika ya riga ya sami sassauci. Wato halin da kasashen Sudan da Liberiya da Burundi da Angola da sauran kasashe masu jawo hankulan mutane suke ciki su ma sun sami sassauci. Daga dukan fannoni, musamman ma daga arewacin Afrika da kudancin Afrika, ana iya gano cewa, ana kasancewa cikin halin zaman karko cikin dogon lokaci, kuma ana more fa'idar zaman lafiya. Game da hargitsin da ake yi, yawancinsu aka yi ne a tsakiyar Afrika da yammacinta, wato a cikin wasu kananan kasashe.

Muhallin zaman lafiya da zaman karko da ake ciki ya samar wa kasashen Afrika dama mai kyau wajen samun bunkasuwar tattalin arziki. Malama He Wenping ta bayyana cewa, tun daga tsakiyar shekaru 90 na karnin da ya shige har zuwa yanzu, a hakika dai ne tattalin arzikin kasashen Afrika yana kara karuwa ya ke yi, dukan mutanen da suka taba sa kafa a kasashen Afrika sun iya gano cewa, babban yankin nan yana kasancewa cikin halin kara samun arziki da wadatuwa sosai, musamman ma jama'ar Afrika da shugabannin kasashensu, dukansu suna fatan kasashen Afrika za su kara samun bunkasuwa.

A watan Yuli na shekarar da muke ciki, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya kimanta cewa, a shekarar da muke ciki, yawan tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 3.6 cikin dari, amma a cikin 'yan shekaru goma da suka wuce, tattalin Arzikin kasashen Afrika ya kara samun karuwa da kashi 3.7 cikin dari, wasu kasashe ma sun samu karuwa da kashi 6 cikin dari. Malama He Wenping ta kara da cewa, da farko, sun samu zaman karko wajen harkokin siyasa. Na biyu, sun sami sakamako daga wajen daidaita tattalin arziki a dukan fannoni, na uku, sun sami taimako daga wajen karuwar tattalin arzikin duniya, musamman ma farashin danyun kayayyaki ya kara hauhawa da saurin gaske, saboda haka, kasashen Afrika sun sami fa'ida daga wajen hauhawar farashin danyun kayayyaki, sa'anan kuma, cinikayyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana kara samun bunkasuwa da saurin gaske, wannan shi ma ya ba da babban taimako ga raya tattalin arzikin kasashen Afrika da saurin gaske a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce.

Kodayake kasashen Afrika suna fuskantar kalubale iri iri, amma mutane suna iya sa ran alheri ga makomar samun bunkasuwar kasashen Afrika.(Halima)