Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-23 19:18:08    
Kabilar Dawo'er ta kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Dawo'er ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Mun je kauyukan kabilar Zhuang don ganin al'adun gargajiya na kabilar wajen wakoki. To, yanzu ga bayanin.

An fi samun 'yan kabilar Dawo'er a cikin jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai da kuma birnin Qiqiha'er na jihar Heilongjiang ta kasar Sin, ban da wannan kuma wasu suna da zama a cikin jihar Xinjiang. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Dawo'er ya kai fiye da dubu 130. 'Yan kabilar suna yin amfani da harshen Dawo'er, amma ba su da harafinsu, yawancinsu suna yin amfani ne da harshen kabilar Han, wasu kuwa suna yin amfani ne da harsunan kabilun Man da Mongolia da kuma Kazakstan.

An 'yantar da 'yan kabilar Dawo'er a cikin shekara ta 1945, kuma an yi gyare-gyaren gonaki a cikin yankunan sha'anin noma a cikin shekara ta 1947, ban da wannan kuma an gudanar da tsarin mallakar filayen makiyaya a yankunan makiyayai, 'yan kabilar sun iya kiwon dabbobi cikin 'yanci. Tun bayan shekara ta 1952, bi da bi ne an kafa kauyukan kabilar Dawo'er guda bakwai a Woniutu da ke bayan birnin Qiqiha'er da kuma Gua'erbenshe'er da ke cikin gundumar Tacheng ta jihar Xinjiang. A watan Agusta na shekara ta 1958, an kafa gundumar Molidawa ta kabilar Dawo'er mai cin gashin kai a cikin jihar Mongolia ta gida, sabo da haka 'yan kabilar sun samu hakkin gudanar da harkokinsu da kansu. 'Yan kabilar Dawo'er da ke bin hanyar gurguzu sun samu bunkasuwa kan tattalin arziki da al'adu cikin sauri, kuma an kyautata zaman jama'ar kabilar sosai. A cikin wadannan shekaru fiye da 50 da suka gabata, an raya sha'anin al'adu ga aikin koyarwa da kiwon lafiya sosai, gundumar kabilar mai cin gashin kai ta kafa makarantar sakandare fiye da 50, matasa da yawansu ya zarce dari sun shiga jami'ai, ban da wannan kuma masu ilmi da ma'aiktan gwamnatin kasar Sin na kabilar suna bayar da gudummowarsu a cikin ayyukansu.