Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-22 18:25:06    
Kasar Sin sahihiyar abokiya ce ta kasashen Afirka

cri

Yayin da shugaban zartaswa na kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Nijer Mamadou Tandja ke zantawa da manema labarai na kasar Sin a kwanan nan, ya bayyana cewa, kasar Sin sahihiyar abokiya ce ta kasashen Afirka, kuma taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi zai samar da dama ga takaita hadin gwiwa cikin sahihanci da ke tsakanin Sin da Afirka a shekaru 50 da suka gabata, da kuma tsara shirye-shiryen samun bunkasuwa a nan gaba.

Kuma shugaba Tandja yana ganin cewa, wannan taron koli wani muhimmin taro ne, kuma ya yi imani cewa, taron zai samu nasara sosai.

Ban da wannan kuma ya bayyana cewa, kasashen Afirka sun dauki kasar Sin tamkar wata sahihiyar abokiya. Kuma sun amince da ra'ayin da kasar Sin ke tsayawa wajen samun daidai wa daida tsakanin kasa da kasa da kuma jama'a da jama'a, da sa kaimi ga kafa odar yin cinikayya tsakanin kasa da kasa cikin adalci, da kuma kulla huldar da ke tsakanin kasa da kasa bisa tushen girmama wa juna. Bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin cikin sauri ta ba wa kasashen Afirka kwarin gwiwa. Kuma dukkan kasashen duniya sun ji mamaki sosai ga nasarorin da Sin ta samu.

Game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijer, shugaba Tandja ya bayyana cewa, an kulla huldar da ke tsakanin kasashen biyu bisa tushen girmama wa juna da amincewa da juna, kuma yanzu ana raya huldar da kyau sosai. Ban da wannan kuma ya darajanta hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijer a fannonin noma da kiwon lafiya da makamashi da kuma albarkatun kasa.(Kande Gao)