
A ran 20 ga wata a birnin Xiamen, an rufe taron bajen koli na nune nunen nasarorin da gabobi biyu na zirin Taiwan suka samu a fannonin aikin gona cikin hadin gwiwarsu da kuma taron gabatar da ayyuka, yawan kudin da aka samu bisa yarjejeniyoyi da aka daddale a gun taron ya kai kudin Sin kusan Yuan biliyan 18 da miliyan 600.
A cikin wadannan kwanaki biyu da aka gudanar da taron, bangarorin biyu sun daddale yarjejeniyoyi a kan ayyukan aikin gona da yawansu ya kai kusan dari 5.
Ofishin harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin da hukumar da abin ya shafa na jam'iyyar Kwamintang ta kasar Sin sun shirya taron cikin hadin gwiwa, wannan taro kuma ya zama wani sashe mai muhimmanci na dandalin tattaunawar hadin kai a kan aikin gona a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan. Wakilai kimanin dubu 4 da suka zo daga gabobi biyu sun halarci taron, wanda ya fi girma bisa mataki dangane da mu'amala da hadin kai da gabobi biyu na zirin Taiwan suka yi a tarihi.(Danladi)
|