Wakilin Kamfanin dillancin labarum Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , tun daga shekarar 1999 , manoman Birnin Baoding na Lardin Hebei na kasar Sin suka fara zuwa kasashen Afrika don samun aikin yi . A cikin shekaru 7 da suka shige, yawan manoman da suke aikin noma da kasuwanci da ciniki a kasashen Afrika ya riga ya kai fiye da 7000 .
Bisa bayanin da aka yi , an ce , lokacin da manoman birnin Baoding suke noman kayan lambu da shinkafa da alkama da masar, wasu daga cikinsu kuma 'yan kasuwa ne, yayin da wasu kuma suna aikin gyare-gayren na'urori . Yanzu sun riga sun kafa Kauyen Baoding 28 a kasar Zambia da Kenya da Habasha da sauran kasashe 14 na Afrika .
Bisa labarin da aka bayar , an ce, gwamnatocin kasashen Afrika suna maraba da Kauyen Baoding , saboda manoman kasar Sin sun samu na'urori da fasahohi na zamani kuma sun samar da abinci da wadatuwa ga Afrikawa. (Ado)
|