Kuna sane da, cewa za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Afrika da kuma zama na uku na ministocin dandalin tattaunawar a watan gobe a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Gwamnatin kasar Zimbabwe da ke can nesa wato kudancin Nahiyar Afrika ta mai da hankali sosai kan wannan taro. Shugaban kasar nan zai ja ragamar tawagar wakilai da za ta kunshi ministoci da yawa zuwan nan kasar Sin domin halartar taron. Kafin wannan lokaci, ministan harkokin waje Mr. Simbarashe Mumbengewi na kasar nan ya karbi ziyarar da wakilinmu ya yi masa, inda ya fadi albarkacin bakinsa kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Nahiyar Afrika da kuma tsakanin kasar Sin da ta Zimbabwe.
Mr. Mumbengewi ya furta, cewa kasar Zimbabwe da kuma kasashen Nahiyar Afrika suna begen ganin bude dandalin tattaunawa ta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Afrika ; ya kuma hakkake, cewa kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa dake kasancewa tsakanin bangarorin biyu wato Sin da Afrika za ta iya kara samun ingantuwa da yalwatuwa. Sa'annan Mr. Mumbengewi ya fadi, cewa 'Wannan ne karo na farko da shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika za su zauna gu daya domin tattauna huldar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma al'amuran duniya. Kasar Sin, kasa ce mai tasowa kuma mafi girma a duniya, kuma ya kasance da akasarin kasashe masu tasowa na duniya a Nahiyar Afrika. Lallai kara kyautata huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin hadin gwiwar tsakanin kasashe masu tasowa yana da muhimmancin gaske'.
Kasar Zimbabwe, ni'imtacciyar kasa ce mai kyan gani. Ta kulla kyakkyawar dangantakar deplomasiyya tare da kasar Sin tun da ta samu mulkin kai a shekarar 1980. Mr. Mumbengewi ya yi waiwayen zumuncin al'ada dake tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe yayin da ya nuna sahihiyar godiya ga kasar Sin bisa tallafin da ta yi mata a fannin kayayyaki da na mutumtaka lokacin da take sanya gwagwarmayar neman mulkin kan al'ummar kasar.
Daga baya, Mr. Mumbengewi ya yi Allah wadai da sambatun banza da wassu kasashen Yamma suka yi cewar wai hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika irin sabon salon ra'ayin mulkin mallaka ne. Ya kuma tabbatar da, cewa su wadannan kasashen Yamma suna duba huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ne bisa ra'ayin 'yan mulkin mallaka. Ya kuma kara da, cewa : ' Lallai shirme ne kasashen Yamma suka yi domin ba su san komai ba game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa na Nahiyar Afrika. Kasar Sin da kasar Zimbabwe da kuma sauran kasashen Afrika aminai ne masu zaman daidaici, wadanda kuma suke hadin gwiwa tsakaninsu da kuma samun moriyar juna ; Amma a nasu bangaren, wassu kasashen Yamma sukan wawwashe albarkatan kasashen Afrika. Ko shakka babu mugun laifi ne suke yi tare da bayyana tarihinsu na mulkin mallaka'.
Kazalika, Mr. Mumbengewi ya yi hasashen, cewa ya kamata kasashen Sin da Zimbabwe su kara yin hadin gwiwa tsakaninsu domun samun bunkasuwa tare. Ya fadi, cewa : 'Muna fatan bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannin siyasa, da tattalin arziki da kuma al'adu da dai sauran fannoni. Kuma muna so mu sanya matukar kokari tare da kasar Sin wajen tabbatar da samun bakin zaren daidaita al'amuran kasa da kasa ta hanyoyi da dama. Babu tamtama, kasashen Sin da Zimbabwe za su hada kan sauran kasashe masu tasowa domin tsayawa kan adalci tsakanin kasa da kasa da kuma yin watsi da akidar nuna kasaita da fin karfi'. ( Sani Wani )
|