Aminai makaunatai, kuna sane da, cewa a cikin mutane da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan dari uku na kasar Sin, kimanin miliyan dari tara ne suke zaune a kauyukan kasar. Har kullum gwamnatin kasar Sin takan mayar da aikin kyautata lafiyar jikin manoman kasar a matsayin wani muhimmin aiki da take yi. Tare da kusantowar ranar bude taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, sassan wasannin motsa jiki na kasar Sin na fatan daga ayyukan wasannin motsa jiki na manoman kasar zuwa wani sabon mataki duk bisa kyakkyawar damar shirya taron wasannin Olympic.
Kwanakin baya ba da dadewa ba, babbar hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta kira wani taron watsa labarai a nan birnin Beijing, inda ta bayyana yadda ake gudanar da harkar ' Yin wasan motsa jiki na dukan jama'a tare da shirye-shiryen wasannin Olympic' a halin yanzu. Mataimakin shugaban babbar hukumar nan Mr. Feng Jianzhong ya fadi, cewa manufar harkar nan, ita ce sa kaimi ga jama'ar kasar Sin wajen nuna himma da kwazo don shiga wasannin motsa jiki da kuma tabbatar da hasashen wasannin Olympic. Yanzu, ana fi bada muhimmanci wajen gudanar da wannan harka a maka-makan kauyukan kasar Sin.
Mr. Feng Jianzhong ya ci gaba da ,cewa akasarin mutanen kasar Sin suna zama a kauyuka. Saboda haka, sai dai manoma mafiya yawa suka shiga cikin wannan harka ne za a iya yadada da kuma ilmantar da kowa daga jama'ar kasar Sin kuma za a iya fadi cewa dukkan mutanen kasar na shiga ayyukan wasannin motsa jiki na Olympic.
Jama'a masu saurare, cikin dogon lokaci ne akan kasa mai da hankali wajen gudanar da ayyukan wasannin motsa jiki a kauyuka yayin da ake yadada harkar yin wasannin motsa jiki na duk kasar kasar Sin. Da yake tattalin arzikin kauyukan kasar suna baya-baya a kwatance, shi ya sa ake karancin muhimman ayyukan wasannin motsa jiki. Hakan ya kawo cikas ga manoman kasar Sin wajen shiga cikin harkar wasannin motsa jiki.
Game da wannan magana, Mr. Feng Jianzhong ya furta, cewa a gabannin ranar bude taron wasannin Olympic, sassan kula da harkokin wasannnin motsa jiki na kasar Sin za su yi amfani da wannan kyakkyawar dama wajen bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na karawa da na jama'a kamar yadda ya kamata, ta yadda za a canza halin koma baya na rashin samun wuraren yin wasannin motsa jiki domin manoma.
Tun daga wannan shekara, gwamnatin tsakiya da kuma gwamnatoci na wurare daban daban na kasar Sin sun riga sun kara daukar matakin gina muhimman ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a, musamman ma sabon yanayi ya bullo a wassu larduna masu hannu da shuni na kasar Sin a fannin ayyukan wasannin motsa jiki na manoman kasar.
A matsayin wani lardi dake cikin sahun gaba a fannin bunkasuwar tattalin arzikin kauyukan kasar Sin, lardin Jiangsu dake gabashin kasar ya fito da cikakken shirin bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na manoma. Mr. Li Yining, shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta lardin Jiangsu ya bayyana, cewa ya zuwa shekarar 2010, za a cimma manufar "kasancewar dakuna da filayen wasannin motsa jiki a kowane kauye" a fadin duk lardin daga dukkan fannoni.
Mr. Li Yining ya hakkake, cewa gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing da za a yi, labuddah zai kara jawo hankulan dimbin jama'ar kasar musamman ma na manoman kasar. Gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing, ya kasance tamkar wata kyakkyawar dama ta ingiza yunkurin bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na kauyukan kasar Sin.
Jama'a masu saurare, mun samu labarin, cewa a shekarar da muke ciki, babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta tsaida kudurin, cewa nan da shekaru biyar masu zuwa, za a gudanar da " Ayyukan wasannin motsa jiki na manoma" a duk kasar baki daya. Muhimmin makasudin ayyukan, shi ne za a gina dakuna da filayen wasannin motsa jiki na jama'a a wassu kauyukan kasar a kowace shekara; Ban da wannan kuma, kawo shekarar 2010, akwai manoma da yawansu ya kai miliyan 150 na kashi daya daga cikin kashi shida na fadin kasar za su samu gajiya daga wannan matakin da aka dauka, ta yadda za a kafa wani irin kyakkyawan tsarin hidima ga dimbin manoma a fannin wasannin motsa jiki.( Sani Wang )
|