Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-19 16:29:47    
Kasar Sin ta horar da kwararru 'yan Afirka fiye da dubu 10

cri

Ya zuwa karshen watan Agusta na shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta riga ta horar da kwararru na fannoni daban daban fiye da dubu 11 da suka zo daga kasashen Afirka fiye da 50.

Wakilinmu ya samu wannan labari ne daga ma'aiktar kasuwanci ta kasar Sin a ran 19 ga wata.

Har kullum kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yin cudanya da hadin gwiwa tsakaninta da mutanen kasashen Afirka, da kuma kara kwarewar Afirka wajen gina kasa ta shirya kwas din horaswa, ta yadda za ta taimake su wajen samun dauwamammiyar bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Kuma wani jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekaru da dama masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a fannin raya 'yan kwadago bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za ta ci gaba da bayar da gudummuwarta kan bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen Afirka.(Kande Gao)