Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-19 15:23:13    
Bayyanin kan Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 na Lardin Heilongjiang(A)

cri

A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani mai lakabin haka: Bayyanin kan Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 na Lardin HeiLongjiang.

A farkon 'karni na 21 , kasar Sin ta kafa cikakken tsarin tattalin arziki na kasuwancin gurguzu . Kuma ta fara shiga cikin muhimmin lokaci don tabbatar da tsarin musamman na 3 . A cikin wannan lokaci . Lardin Heilongjiang ya kyautata fasalin tattalin arzikinsa . Kuma ya kara saurin bunkasa tattalin arziki da ci gaban zaman al'umma . Gwamnatin Lardin Liaoning ta tsara kuma tana aiwatar da Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 kan tattalin arziki da zaman al'umma na Lardin Liaoning . Wannan shirin yana da babbar ma'ana a tarihance .

Lardin HeiLongjiang yana daya daga cikin larduna 3 dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin dake karkashin gwamnatin kasar Sin .

Lardin Heilongjiang yana da wadatattun albarkatu . Fadin gonakai ya kai muraba'in kadada dubu 2800 , wato ya kai kashi 7 cikin 100 na duk fadin kasar Sin . A Lardin Heilongjiang ana iya bunkasa aikin noma da masana'antun man fetur da kuma masana'antun harhada magunguna.

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , Saboda tattalin arzikin kasar Sin ya sami bunkasuwa da saurin gaske kuma cikin dogon lokaci , shi ya sa a cikin 'yan shekarun da suka wuce , a nan kasar Sin aka fuskanci halin 'karancin wutar lantarki wanda ba a taba ganinsa ba a tarihi . A yanayin zafi na wannan shekara , galibin wuraren kasar Sin suna fuskantar halin karancin wutar lantarki . Saboda haka Wurare daban daban na Kasar Sin za su dauki matakai masu yawa don rage tsananin matsalar karancin wutar lantarki , kuma a kan manufar tabbatar da yawan wutar lantarkin da ke samarwa ga zaman yau da kullum na jama'a , za a biya bukatun sassa daban daban na zaman al'umma a wajen yin amfani da wutar lantarki .

A watanni 3 na farko na wannan shekara , yawan tashoshin ba da wutar lantarki na larduna wadanda suka dauki matakan kayyade yawan amfanin wutar lantarki ya kai 26 . Lardin Heilongjiang yana daya dake cikinsu . Daga karshen watan Yuni , wurare Masu yawa na kasar Sin sun fuskanci yanayi mai zafi sosai, abin da ya yi sanadiyyar 'karuwar amfani da wutar lantarki . Alal misali a Lardin Heilongjiang , yawan wutar lantarkin da aka yi amfani a wajen bude iyakwandishin ya kai kimanin kashi 40 cikin 100 na jimlar wutar lantarkin , saboda haka an kara sabanin samar da wutar lantarki . Kamfanin ba da lantarki na kasar Sin ya kimanta cewa , a yanayin zafi na wannan shekara a duk kasar za a fuskanci karancin lantarki na kilowatt miliyan 25. Don rage halin karancin wutar lantarki da tabbatar da aikin samar da wutar lantarki , wurare daban daban na kasar Sin sun dauki matakai masu yawa . Lardin Heilongjiang yana daya daga cikinsu.

Li Zongguo , kakakin watsa labaru na Kamfanin ba da wutar lantarki na Lardin Heilongjiang ya bayyana cewa , tun daga watan Satumba na shekarar bara , kamfaninsa ya fara aikin share fagen samar da wutar lantarki a wannan shekara .

Mr. Li ya ce , mun tattara kudin Sin Yuan fiye da biliyan 2 don kyautata manyan ayyukan ba da wutar lantarki , kuma a kafin ran 30 ga watan Yuli na wannan shekara mun gama ayyukan . A yanayin zafi, wadannan ayyukan sun ba da taimako kwarai da gaske .(Ado)