kwanan baya, masu sauraronmu da dama sun yi mana tambayoyi dangane da matan kasar Sin. kamar misali, a cikin wasikar da malama Fatima Sadah daga birnin Zaria na jihar Kaduna ta kasar Nijeriya ta aiko mana, ta ce, wadanne irin gudummowa ne matan kasar Sin suke bayarwa a wajen bunkasa da ci gaban kasar Sin, kuma wadanne sana'o'i ne matan kasar Sin suka fi yi? kuma malama Jamila Adamu mazauniyar jihar Kaduna ta rubuto mana cewa, ko gwamnatin kasar Sin tana taimakawa matan kasar a wajen bunkasa sana'o'insu, shin hukumomin kasar Sin su kan ba mata 'yan kasar rance domin su bunkasa sana'o'insu? shim kamfanonin kasar Sin suna daukar matan kasar Sin aiki. Bayan haka, malama Ladidi Ibrahim S da ke zaune a zaria Kaduna ta tambaye mu, ko akwai kungiyoyin mata 'yan kasuwa a kasar Sin, shin akwai gudummuwar da gwamnati ko hukumar kasar Sin take bayarwa, musamman bayar da basussukan bunkasa sana'o'in mata? To, sabo da haka, bari mu amsa wadannan tambayoyi, mu bayyana muku halin da matan kasar Sin ke ciki.
Matan kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa a wajen bunkasa zaman al'umma, suna kuma ba da babban taimako a wajen bunkasuwar tattalin arziki. Suna ba da muhimmiyar gudummuwarsu a wajen ayyukan masana'antu da noma da kimiyya da al'adu da ilmantarwa da kiwon lafiya da dai sauran harkoki daban daban na raya kasa. A nan kasar Sin, 'rabin duniya' shi ne babban yabon da duk al'umma suka yi wa matan kasar.
Sabuwar kasar Sin ta sanar da cewa, matan kasar Sin suna da hakkokin da suka zo daya da na maza. A bayyane ne tsarin mulkin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ya kayyade cewa, 'mata suna da hakkokin da suka yi daidai da na maza a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma da dai sauransu.' Bayan haka, dokoki daban daban na kasar Sin sun tabbatar da hakkoki da matsayi da mutumci iri daya a tsakanin mata da maza. Gwamnatin kasar Sin ta kuma dauki matakai da dama a fannonin doka da mulki da ilmantawa don neman kawar da bambance-bambancen da aka nuna wa mata da kuma kiyaye moriyarsu.
Matan kasar Sin suna da hakki iri daya da na maza a wajen samun aikin yi. Tun bayan aka kafa sabuwar kasar Sin, matan da suke samun aikin yi sai karuwa suke. A halin yanzu, a nan kasar Sin, yawan matan da suke da aiki ya kai kashi 44% na dukan jama'ar da ke da aikin yi, har ma adadin ya wuce kashi 34.5% na duniya. Ban da wannan, matan kasar Sin suna sana'o'i iri daban daban masu yawa, ciki har da masana'antu da ayyukan noma da gine-gine da sufuri da ciniki da kiwon lafiya da ba da ilmi da dai sauran mukamai na hukumomi ko kungiyoyin al'umma.
Ban da wannan, a kasar Sin, mata suna kokarin kula da harkokin kasa da na zaman al'umma, suna ba da babban taimako a wajen raya dimokuradiyya da dokoki a kasar Sin. Matan kasar Sin suna da muhimmin matsayi a cikin majalisun wakilan jama'ar kasar Sin na matakai daban daban. Mata wakilan jama'a suna taka muhimmiyar rawa a wajen kafa doka da kuma kula da harkokin kasa da na zaman al'umma.
A kasar Sin, mata suna da kungiyoyinsu masu dimbin yawa wadanda yawansu ya wuce 5,800, wadanda kuma su kan sanar da gwamnati a kan ra'ayoyin mata da kuma matsalolin da suke fuskanta tare kuma da bayar da shawarwari. Su muhimman kungiyoyi ne a wajen kiyaye hakkin mata. Daga cikinsu kuma, hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta fi girma. Kungiyar ta kafu ne a shekara ta 1949, kuma babbar manufarta ita ce kiyaye moriyar mata da kuma inganta daidaici a tsakanin maza da mata. Ban da kungiyar, akwai kuma sauran kungiyoyin mata na sana'o'i, kamar su kungiyar mata masu masana'antu da kungiyoyin mata magadan gari da kungiyoyin mata alkalai da dai sauransu.
Game da ko gwamnatin kasar Sin tana taimakawa matan kasar a wajen bunkasa sana'o'insu, E, haka ne. A gun taron matan duniya da aka yi yau da shekaru 10 da suka wuce, a fili ne gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa, za ta mayar da fid da mata daga talauci a matsayin wani muhimmin sharadi a wajen kyautata matsayin mata. A cikin shekaru 10 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta yi ta kokartawa ba tare da kasala ba, kuma ta gabatar da jerin manufofin da za su amfana wa mata kai tsaye. Ciki har da ba da rancen kudi ga mata, don taimakawa wajen bunkasa sana'o'in mata a yankunan da ke fama da talauci, da koyar musu fasahohi don inganta karfinsu na yaki da talauci da dai sauransu. (Lubabatu)
|