Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-18 18:25:19    
Ana kara dankon aminci a tsakanin Sin da kasshen Afrika ta hanyar binciken ilmi

cri
A karo ne na farko, kasar Sin ta bayar da "takardar manufofin kasar Sin game da harkokin Afrika" a watan Janairu na shekarar nan, wannan yana da matukar muhimmanci ga gudanar da dangantaka da ke tsakanin Sin da Afrika yadda ya kamata kuma daga duk fannoni, sa'an nan a fili ya nuna manufofin da ake bi a kasar Sin wajen binciken hasashen batutuwan Afrika. A ran 17 ga wata, jaridar kasar Sin da ake kira "People's Daily" ta buga wani bayani da Malam Zhen Feng, shugaban sashen binciken Afrika ta Jami'ar birnin Nanjing ya rubuta.

Bayanin ya ce, binciken ilmi da musayarsa da ake yi ta yi a tsakanin Sin da Afrika a cikin sama da shekaru 10 da suka wuce, ya ba da babban taimako ga gaggauta yalwata dangantakar aminci da kara fahimtar juna a tsakanin Sin da Afrika daga duk fannoni. Jami'ar birnin Beijing da ta birnin Nanjing da sashen binciken ilmi na yammacin Asiya da Afrika na cibiyar nazarin ilmin zaman rayuwar yau da kullum ta kasar Sin da makamantansu suna aikin wurjanjan wajen binciken ilmin Afrika. A halin yanzu, kungiyar binciken batutuwan Afrika ta kasar Sin kungiya ce daya tak da ke binciken batutuwan Afrika daga duk fannoni a kasar Sin. A watan Yuli na shekarar 1979, an kafa kungiyar nan wadda ta alamanta cewa, kasar Sin ta sami ci gaba wajen binciken batutuwan Afrika.

Bayanin ya kara da cewa, a cikin sama da shekaru 20 da suka wuce, kungiyar nan ta gudanar da harkokin kara wa juna sani har fiye da sau 100, ta wallafa makalu dubai da littattafan binciken ilmi da na fassarawa da karamin sani da yawansu ya kai kimanin 100, lalle, ta sami sakamako mai kyau. Littafi mai suna "binciken batutuwan manyan tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Afrika" da aka shirya a karkashin jagorancin kungiyar nan ya sami babban yabo daga wajen kwararru na gida da waje. A lokacin da ake yin babban taron wakilan kungiyar na karo na 7 da aka yi a watan Disamba na shekarar 1992, an taba shirya taron kara wa juna sani a kan kulla danganatar hadin kai tsakanin Sin da Afrika yadda ya kamata kuma a duk fannoni don fuskatar karni na 21. Bayan taron, an wallafa wani littafi mai suna "rahotanni kan manyan tsare-tsaren bunkasa dangantaka a tsakanin Sin da Afrika a karni na 21. A cikin littafin nan, an waiwayi hanyoyi da aka bi wajen kulla aminci da ma'amala a tsakanin Sin da Afrika a fannin siyasa da tattalin arziki da diplomasiya da jam'iyyun siyasa a cikin shekarun nan 50 da suka wuce, kuma an bayyana matukar muhimmacin dangantakar hadin kai a tsakanin Sin da Afrika a karni na 21, an gabatar da ra'ayoyi da shawarwari masu yakini da yawa a kan zurfafa dangantakar aminci da hadin kai a tsakanin Sin da Afrika a cikin sabon zamani, da inganta hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya, da raya kasuwannin Afrika, da kara ma'amalarsu a fannin al'adu da sauransu.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a cikin rabin karni da ya wuce, musamman tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa, an sami babban ci gaba wajen binciken ilmi da yin ma'amala a tsakanin Sin da Afrika, ta haka an gaggauta yalwata dangantaka da ke tsakaninsu yadda ya kamata. Yayin da Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya kai ziyara a nahiyar Afrika a watan Afrilu da ya wuce, ya gabatar da shawarwari guda biyar don ingiza yalwata huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare, wadannan shawarwari su ne, kara amincewa da juna a fannin siyasa, da kara taimakon juna a fannin tattalin arziki don samun nasara tare, da kara koyi da juna a fannin al'adu, da inganta hadin kansu a fannin tsaro, da kuma taimakon juna sosai a duniya. Wadannan shawarwari kuma sun samar da sabuwar dama ga kungiyoyin binciken ilmi na kasar Sin don kara wa juna sani a tsakanin Sin da Afrika. (Halilu)