Lokacin hutu na tsawon kwanaki 7 don taya murnar cikon shekaru 57 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin yana da ma'anar musamman ga 'yan birnin Chongzhou na lardin Sichuan na kasar Sin, saboda an yi wata muhimmiyar gasa ta matsayin duniya wato gasar ba da babbar kyauta ta kasar Sin ta gasar fid da gwani ta duniya ta tseren kananan jiragen ruwa ta F1 a wannan birni a karo na farko a ran 5 ga wata, inda 'yan birnin suka samun damar jin dadin kallon irin gasa ta matsayin koli.
Gasar fid da gwani ta duniya ta tseren kananan jiragen ruwa ta F1 gasa ce da Hadaddiyar Kungiyar Tseren Kananan Jiragen Ruwa ta Duniya wato UIM ta shirya tun daga shekarar 1981, inda 'yan kallo suke jin dadin kallon karawa mai tsanani da ke tsakanin 'yan wasa, suke jin zumudi sosai. A cikin shekarun nan da suka wuce, an taba yin wannan gasa a biranen Hangzhou da Wuxi da Xiamen da kuma Shanghai da ke gabashin kasar Sin, a karo na farko ne an yi wannan gasa a yammacin kasar a wannan shekara.
'Yan wasa gwanaye sun fi iya bayyana ra'ayoyinsu kan gasar fid da gwani ta duniya ta tseren kananan jiragen ruwa ta F1 da aka yi a yammacin kasar Sin, in an kwatanta da sauran mutane. Dan wasa mai suna Scott Gillman daga kasar Amurka, wanda ya zama zakara a wannan gami, ya yaba wa ayyukan shirya wannan gasa, ya bayyana cewa, kasar Sin ta gwanance wajen shirya wannan gasa.
Ko da yake bai sami maki mai kyau ba, amma sharaharren dan wasa mai suna Guido Cappellini daga kasar Italiya da ya taba zama zakara a cikin gasannin da aka yi a biranen Hangzhou da Wuxi ya bayyana cewa, yana son shiga gasar da aka yi a kasar Sin sosai, a sa'i daya kuma, ya nuna yabo ga kishin da kafofin yada labaru suka bayar kan wannan gasa, ya ce,'Ina jin farin ciki domin komawa kasar Sin, saboda na kan taki sa'a a kasar Sin, ina fatan zan taki sa'a a nan gaba. Sa'an nan kuma, Sinawa suna karbar baki da hannu biyu biyu. Hanyoyin wasa da ke Chongzhou suna da kyau, har ma sun zama na matsayin koli a cikin dukan hanyoyin wasa da na taba gani. Kafofin yada labaru na kasar Sin sun nuna gwaninta wajen ya da gasar nan, tallar da suka yi kan wannan gasa suna ko ina.'
Shahararren dan wasa mai suna Chiappe Phillipe daga kasar Faransa da ya wakilci kungiyar kasar Sin ya zama na 7 a wannan gami. Ko da yake kungiyar kasar Sin ba ta taba samun maki mai kyau a cikin gasannin tseren kananan jiragen ruwa ta F1 ba, amma Mr. Phillipe ya wakilci kasar Sin, ya ce, dalilin da ya sa hakan shi ne domin kishin da mutanen Sin ke nunawa kan wannan wasa ya burge shi.
'Yan wasan kasashen waje sun yaba wa shigar yammacin kasar Sin da tsren kananan jiragen ruwa ke yi, yaya ra'ayoyin 'yan wasan kasar Sin? Peng Linwu, wanda aka mayar da shi a matsayin dan wasan kasar Sin ne na farko da ya shiga cikin gasannin tseren kananan jiragen ruwa, ya bayyana cewa,'Ina tsammani cewa, wannan wasa zai ba da babban tasiri kan mutane da yawa, mai yiwuwa ne matasa za su shiga wannan wasa, ko kuma mutane za su yi kallon wannan wasa, ina son ya da sunan wannnan wasa musamman ma iri na F1, ta hanyar watsa labaru a kansa, ta haka mutane za su kara karbe shi, za su kara shiga cikinsa. Yanzu kasarmu ta kyautata zaman rayuwa. Na ji an ce, saboda wannan wasa yana ba da babban tasiri, shi ya sa masana'antu masu yawa suna son ba da kudade domin wannan gasa, ko kuma goyon bayan kungiyoyin tseren kananan jiragen ruwa. A kasashen Turai, wasan nan mai farin jini sosai, yawan 'yan kallo ya fi na kasarmu.'
Ko da yake mutanen Sin kadan ne suka san tseren kananan jiragen ruwa ko kuma shiga cikinsa, amma Mr. Peng ya yi imanin cewa, saboda karuwar karfin kasar Sin, mutanen Sin za su kara shiga cikin wannan wasa, sa'an nan kuma, ya da wasan tseren kananan jiragen ruwa a kasar Sin zai sa kaimi kan bunkasuwar aikin yawon shakatawa na kasar Sin. Ya ce,'A ganina, yana da muhimmanci sosai, da farko, mutane za su iya kallon irin wannan gasa mai saurin haka, na biyu, saboda karuwar karfin kasarmu da karuwar kudin shiga da jama'armu ke samu, mutane da yawa za su mai da hankali kan wasannin kan ruwa. Ina tsammani, wannan zai sa kaimi kan ci gaban aikin yawon shakatawa na kasarmu sosai.'(Tasallah)
|