Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-18 17:08:41    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(12/10-18/10)

cri
Kwanan baya, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya canja sunan abubuwan nuna fatan alheri na taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing FRIENDLIES zuwa FUWA. Wani jami'in kwamitin ya bayyana cewa, FUWA ya fi ba da sauki wajen yayata taron wasannin Olympic na Beijing. Ya kara da cewa, bayan da aka canja sunan abubuwan nuna fatan alheri, za a yi kwaskwarima da canje-canje ga kayayyakin taron wasannin Olympic na Beijing da aka kera bisa izinin musamman da tallar ya da taron wasannin Olympic na Beijing.

Ban da wannan kuma, akwai wani labari da aka samu daga wannan kwamiti a ran 13 ga wata cewa, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya ba da takardun nadi a karo na 3 ga mashawarta 4 masu ilmin harkokin muhalli na kasar Sin. A cikin shekarun nan da suka wuce, wadannan kwararru 4 sun shiga cikin ayyukan taron wasannin Olympic na Beijing da suka shafi muhalli. Bayan da aka ci gaba da nada su, za su kammala ayyukansu bayan taron wasannin Olympic na Beijing da na nasakassu.

Ran 15 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an bude gasar duniya bisa gayyata ta Shanghai ta taron wasannin Olympic na musamman na shekarar 2006. An yi kwanaki 5 ana yin wannan gasa, za a kammala ta a ran 20 ga wata. 'Yan wasa da malaman wasa kimanin 2,000 daga kasashe da yankuna 20 sun shiga ayyukan wasanni 21 a hukunce da kuma wasanni 4 da ba na hukunce ba. Birnin Shanghai ya shirya wannan gasa ne don share fage ga taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi da za a yi a Shanghai a watan Oktoba na shekara mai zuwa. Sa'an nan kuma, mataimakin babban sakataren gudanarwa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na shekarar 2007 Wang Wei ya bayyana a ran 14 ga wata cewa, yanzu ana tafiyar da dukan ayyukan shirya taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na shekarar 2007 yadda ya kamata.

'Yar wasa Sun Weiwei daga kasar Sin ta zama zakara da awoyi 2 da mintoci 34 da dakikoki 36 a tsakanin mata a cikin gasar gudun Marathon ta duniya da aka yi a nan Beijing a ran 15 ga wata. Dan wasa Salim Kipsang daga kasar Kenya ya zama na farko da awoyi 2 da mintoci 10 da dakikoki 18 a tsakanin maza. 'Yan wasa fiye da 20,000 daga kasashe da yankuna 30 sun shiga wannan gasa.(Tasallah)