Masu yawon shakatawa na kasashen waje da suka zo kasar Sin ziyara su kan ce, kai ziyara ga birnin Xi'an don ganin kayayyakin gargajiya na kasar Sin, kuma ziyarar Guilin don ganin tsaunuka da koguna iri na kasar Sin. To, yanzu za mu gabatar muku da sharaharrun wurare masu ni'ima na Guilin, wadanda aka mayar da su a matsayin gaba a duk duniya saboda kyan ganinsu.
Birnin Guilin yana cikin jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai cin gashin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin, shahararren wurin shakatawa ne a duk duniya. Kogin Lijiang mai tsawon kilomita 83, wanda ya tashi daga birnin Guilin zuwa gundumar Yangshuo, ya iya zama wakili ne na wurare masu ni'ima na kasar Sin, saboda tsaunuka da kuma wurare masu ni'ima iri na kauye da ke gabobi 2 sun sanya masu yawon shakatawa su shiga zane-zanen gargajiya na kasar Sin.
A duk dare, a gundumar Yangshuo, a kan kogin Lijiang, 'yan wasan kwaikwayo fiye da 600 sun hada kansu su nuna wani kasaitaccen wasan kwaikwayon rawa da waka, wanda aka samar da shi bisa labarin wani budurwa mai suna Liu Sanjie.
An yi amfani da tsaunuka da kogin Lijiang da sauran wurare masu ni'ima wajen nuna wannan wasan kwaikwayo kai tsaye. Yawancin wadannan 'yan wasan kwaikwayo ba kwararru ba ne, su ne 'yan kauye. A cikin wannan wasan kwaikwayo, an bayyana zaman rayuwar masunta da ke zama a gabobi 2 na kogin Lijiang da kuma halin musamman na kananan kabilu da ke zama a wannan yanki, kamar su kama kifi da kiwon shanu da noman shuke-shuke da almara da wakokin gargajiya na kabilar Zhuang.
Tun bayan da aka fara nuna wannan wasan kwaikwayo a watan Oktoba na shekarar 2003 har zuwa yanzu, ana nuna shi a kalla sau daya a ko wace rana, mutane sun yi kishin kallonsa sosai.
Malam Thomas Laubis da matarsa Martina, 'yan kasar Jamus, sun zo Yangshuo ziyara, sun nuna babban yabo ga wannan wasan kwaikwayo na rawa da waka. Wannan shi ne karo na farko da suka zo kasar Sin ziyara. Ko da yake sun yi yini daya suna Yangshuo, amma ba su so koma gida saboda kyan ganin Guilin.
Mr. Thomas Laubis ya ce,
'Wurin nan na da matukar kyan gani, tabbas ne ziyarar da muke kawo wa kasar Sin a wannan gami ba ziyara ba ce ta karshe da za mu kawo wa kasar Sin ko kuma kasashen Asiya.'
Madam Martina Laubis ta ce,
'mutanen wurin suna da kirki, su kan yi hira da mu, a ganina, na iya amincewa da su. Tabbas ne za mu sake zuwa kasar Sin, za mu kai ziyara ga sauran wuraren kasar.'
Kamar yadda bakin kasar Jamus suka fada, wurare masu ni'ima na Guilin da ba a taba ganin irinsu a sauran wurare ba sun jawo dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje.
Ban da masu yawon shakatawa na kasashen waje kuma, wasu shugabanni da manyan jami'an kasashen waje su kan kai wa Guilin ziyara a lokacin da suke ziyarar kasar Sin. Har zuwa yanzu shugabannin kasashen waje 108 sun taba ziyarar Guilin.
A wurare da yawa na duniya, bunkasuwar aikin yawon shakatawa da kuma karuwar masu yawon shakatawa sun matsa babbar lamba ga muhalli na wurin, har ma sun kawo illa. Amma Guilin bai bi irin hanya ba. Iska da ruwa na da tsabta a nan. Mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta birnin Guilin Mr. Chen Yunchun ya yi bayani kan wannan cewa, don kiyaye muhalli yadda ya kamata, birnin Guilin ya mayar da kiyaye muhalli a gaban kome. Yana raya wurare masu ni'ima na Guilin amma tare da sharadi na farko, wato kiyaye su. Ya ce, (murya ta 5, Chen)
'gwamnatin birninmu ta mayar da kiyaye muhalli a gaban kome. Ko kusa ba mu goyi bayan shirye-shiryen yawon shakatawa ba, idan ba a amince da su a fannin kiyaye muhalli ba. Yanzu birnin Guilin ya bunkasa masana'antu na zamani, a maimakon masana'antun da suka samar da bakin hayaki ko kuma suka gurbata muhalli.'(Tasallah)
|