Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-17 20:38:04    
Karamin tsibiri na Gulangyu

cri

An mayar da karamin tsibirin Gulangyu tamkar lambun da ke cikin teku. Fadinsa ya kai murabba'in kilomita 1.84, inda mutane 20,000 suke zama a kansa. Kogin Lu ya raba shi daga birnin Xiamen na kasar Sin. Nisan da ke tsakanin wannan karamin tsibiri da Xiamen ya kai mintoci 10 kawai a cikin jirgin ruwa a kudu maso yammaci. Saboda kasar Birtaniya ta taba mayar da shi a matsayin daya daga cikin tashoshin cinikinta a shekarar 1842, shi ya sa har zuwa yanzu an iya ganin manyan gine-gine da coci da sito-sito da gine-ginen gwamnati iri na salon kasashen yamma a wannan karamin tsibiri.

Akwai wani babban dutse mai tsawon mita 92.6 a cibiyar karamin tsibirin Gulangyu, an kuma sassaka mutum-mutumin Zheng Chenggong a kansa, wanda wani jarumi ne na kasar Sin na zamanin da a sakamakon sake dawowa da tsibirin Taiwan daga hannun 'yan kasar Holland, 'yan mulkin mallaka a shekarar 1661. An kuma gina wani dakin tunawa don tunawa da gudummuwar da ya bayar. Masu yawon shakatawa sun iya hangen shudin ruwan teku da ke kewayen tsibirin da rairayin bankin teku mai launin zinare da gine-gine iri daban daban da kuma dimbin furanni da tsire-tsire a nan.

Karamin tsibirin na Gulangyu ya yi suna ne tamkar tsibiri na kide-kide. Gini mafi burge mutane da ke cikin wadannan gine-gine iri na salon mulkin mallaka a wannan karamin tsibiri shi ne dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Xiamen, wanda aka gina shi a kan wani karamin tuddu. Kubbarsa mai launin ja. An sassaka ramuka a cikin hanyoyin da ke cikin dakin, ta haka an iya amsa kuwwar matakan mutane. Ana nuna kayayyakin gargajiya iri fiye da 1,000, kamar su fadi-ka-mutu da lu'ulu'u. Idan aka hange nesa daga wannan dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya, wannan karamin tsibiri ya yi kama da wani teku na kwarran itatuwa da kuma jan rufi.

Karamin tsibirin Gulangyu yana gudu daga motoci da kuma basukur, masu yawon shakatawa suna iya jin amon biyano mai dadin ji daga wasu kusurwoyi masu shiru, wadanda ke bayan itatuwa, ta haka an tuna da masu yawon shakatawa wani suna daban na wannan karamin tsibiri mai kyan gani, wato tsbiri na biyano.(Tasallah)