Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-17 15:57:29    
Ministan ciniki da masana'antu na Kenya ya yi babban yabo ga dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri
Za a bude dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a nan Beijing a farkon watan Nuwamba. A kwanan baya, ministan ciniki da masana'antu na kasar Kenya Mukhisa Kitui ya yi babban yabo ga wannan dandalin tattaunawa saboda inda ya ce, dandalin yana taka rawa mai yakini wajen raya kasar Sin da kasashen Afirka.

Mr. Kitui ya bayyana cewa, tattaunawa tsakanin Sin da Afirka tana da muhimmanci sosai, dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya samar da wani nagartaccen dandali ga dukan bangarorin 2. Wadannan kasashe masu tasowa za su kara karfinsu saboda yin koyi da juna.

Ya kara da cewa, a gun dandalin da za a yi a wannan gami, bangarorin Sin da Afirka za su tattauna yadda za a sa kaimi kan shawarwari na zagaye na Doha da kuma yadda za a ingiza bunkasuwar tattalin arzikinsu ta hanyar bunkasa cinikin da ke tsakaninsu, a cikin halin da ake ciki a yanzu, wato ana gamuwa da matsaloli wajen tafiyar da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban.(Tasallah)