Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 21:39:09    
Kasar Sin ta soke basussukan da yawansu ya kai yuan biliyan 10.9 na kasashen Afirka 31

cri
A yau ranar 16 ga wata, a yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru, Chong Quan, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, kuma kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar, ya ce, bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kasar Sin ta soke basussukan da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 10.9 da take bin kasashen Afirka 31 wadanda suka cin bashi mafi yawa kasashe ne da suka fi fama da talauci.

Mr.Chong Quan ya ce, tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a shekara ta 2000, don taimaka wa kasashen Afirka a wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, bi da bi ne gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da jerin manyan matakai wadanda ke da nufin inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afirka. Ban da yafe musu basussukan da suka ci, ta kuma soke kudin kwastan a kan wasu kayayyakin da kasashen Afirka 28 mafi rashin samun ci gaba suke fitarwa zuwa kasar Sin, ta kuma horar da kwararru iri iri da yawansu ya wuce dubu 10 ga kasashen Afirka. Ban da wannan, ta kuma sa kaimi ga kamfanoni masu karfi da su je Afirka don zuba jari da kuma kafa masana'antu. Ya zuwa yanzu dai, kudaden jari da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya riga ya zarce dallar Amurka biliyan 6.2 gaba daya.(Lubabatu)