Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 16:23:23    
Kungiyoyin ba da agaji na Red Cross da ke kauyukan kasar Sin

cri

Bisa matsayinta na wata kungiyar jiyya ta jama'a, har kullum kungiyar ba da agaji ta Red Cross tana dukufa kan ba da taimakon agaji ga 'yan gudun hijira da masu fama da bala'i. Ban da wannan kuma ta kan shiga harkokin jin kai cikin yakini. An kafa kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin a shekara ta 1904, ya zuwa yanzu, kungiyar tana da rassa 31 bisa matsayin lardi da kuma rassa biyu bisa matsayin shiyyar musamman ta kasar Sin wato Hongkong da Macao. Bugu da kari kuma kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin tana da kananan kungiyoyin jiyya da ke karkashin jagorancinta fiye da dubu 70.

A cikin gundumar Jinshang da ke birnin Shishi na jihar Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin, akwai wata karamar kungiyar ba da agaji ta Red Cross wadda ba ta gwamnati ba. Fararren hula na wurin da suke son sha'anin jin kai su kansu ne suka kafa kungiyar, kuma suka tattara kudi da kayayyakin kyauta daga fararren hula domin gudanar da harkokin jin kai, sabo da haka ne fararren hula na wurin sun nuna mata aminci sosai. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan kungiyar ba da agaji ta Red Cross.

Gundumar Jinshang ta birnin Shishi wata karamar gunduma ce da ke bakin teku. Yawan mazaunan gundumar bai kai dubu goma ba, amma yawan sinawa 'yan kaka gida na wurin ya zarce dubu goma. Matsakaicin yawan kudin da mazaunan wurin suke samu a ko wace shekara ya kai dubu takwas. Amma a wannan wurin inda tattalin arzikinsa ya samu ci gaba a gwargwado, kuma zaman rayuwar mazaunan ya samu wadata, wasu mutane su kan fuskanci mawuyacin hali yayin da suka kamu da cututtuka ko kuma gamu da bala'i daga indahalli, kuma su kan bukaci kulawa da taimako daga al'umma.

A wata rana ta shekara ta 1999, wani al'amari ya burge Wu Qichang sosai, wanda ya bude wani kantin buga rubutu a gundumar. Wani dan kauye da ke fama da talauci ya roki Mr. Wu da ya rubuta wata wasika zuwa ga danginsa domin neman taimakon kudi don yin wa mahaifiyarsa jiyya. Daga baya kuma Mr. Wu ya fahimci cewa, wannan dan kauye ba shi da kudi sam, har ma ba shi da kudin sayen kananzir domin kunna fitila. Sabo da haka, wani tunani kan kafa wani asusun ba da agaji ya fado masa a zuciya. Ya bayyana cewa,

"na gamu da tsofaffi da yawa, wadanda su kan roke ni da na rubuta masu wasiku zuwa ga dangoginsu a kasar Philippines da kuma shiyyar Hongkong ta kasar Sin don neman samun wasu kudade, ta yadda za a iya fitar da su daga mawuyacin halin da suke ciki. Sabo da haka na gano cewa, a cikin wurare masu ci gaba, akwai wasu mutanen da ke bukatar taimakon da aka ba su."

Tunanin nan na Wu Qichang ya yi daidai da na Qiu Yushang, wani soja da ya riga ya yi ritaya. A karkashin kokarinsu, a ran 17 ga watan Janairu na shekara ta 2001, aka kafa kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta gundumar Jinshang. Kuma bayan kafuwar kungiyar ba da dadewa ba, sun yi wasu abubuwan da ke jawo hankulan mazaunan wurin sosai.

Qiu Yunying, wata yarinya ce mai shekaru shida da haihuwa, ta sami kari sama da goma a jikinta wadanda girman ko wanensu ta yi daidai da kwai, har kullum ba ta iya yin barci sakamakon jin zafi. Ganin haka Qiu Yushang da sauran mutanen wurin sun yi iyakacin kokarinsu domin tattara kudi domin yi wa Qiu Yunying tiyata. Qiu Yushang ya bayyana cewa,

"za a yi wa Yunying tiyata, amma ba ta da kudi. Dagacinmu yana fatan kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta gundumar za ta iya samar da taimako. Sabo da haka, mun shirya wani akwatin tattara kudin taikamo, kuma mun je wurare daban daban domin neman fararren hula su ba ta taimakon kudi, a karshe dai mun tattara kudi yuan fiye da dubu 110 da 500 gaba daya."

Tun bayan shekara ta 2001, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta gundumar Jinshang ta riga ta tattara kudin kyauta har yuan fiye da dubu 400, da kuma bayar da taimako ga masu fama da bala'i da talauci har sau 30. Ta haka mutane fiye da 3000 sun amfana daga kungiyar.

Tare da bunkasuwar sha'anin jiyya na kungiyar, yawan membobin kunigyar jiyya ta Red Cross ta gundumar Jinshang ya karu daga 37 zuwa 212. A cikinsu, akwai manoma da 'yan kasuwa da 'yan kwadago wasu daga cikinsu suna da kudi yayin da wasu ba su da kudi, amma dalilin da ya sa suka shiga kungiyar daya ne, wato suna son nuna kauna ga mutanen da ke bukatar taimako. Cai Shengli, wani membar kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta gundumar Jinshang kuma wani dan masana'anta mai zaman kansa ya bayyana cewa,

" mutum guda daya bai iya samar da kudin da aka bukata ba, idan ana so a tattara mutane da yawa domin bayar da gudummowa ga jama'a, ba yadda za a yi sai a dogara da kungiyar ba da agaji ta Red Cross."

Yanzu dukkan membobin kungiyar suna bayar da gudummowarsu bisa kaunar da suka nuna wa sauran mutane ba tare da nadama da yin gunaguni ba.(Kande Gao)