An fi samun 'yan kabilar Korea a jihohin Hei Longjiang da Jilin da Liaoning na kasar Sin. Ban da wannan kuma wasu 'yan kabilar suna da zamansu a cikin jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai da biranen Bijing da Shanghai da Hanzhou da sauran manyan biranen kasar Sin. 'Yan kabilar da ke da zama a yankin Yanbian mai cin gashin kai na jihar Jilin suna magana da harshen Korea kuma yin amfani da harafin Korea, kuma 'yan kabilar da ke cikin sauran wurare suna yin amfani da harafin kabilar Han. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Korea ya kai miliyan 1.9.
Bayan da kasar Sin ta ci nasarar yakin fama da mahara Japanawa a cikin shekara ta 1945, yankunan kabilar Korea sun samu 'yancin kai daya bayan daya, haka kuma a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an kafa muklin kai na jama'ar kabilar. A cikin shekara ta 1946, an yi gyare-gyaren gonaki. Bayan kafuwar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, musamman ma bayan taro na uku na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi a cikin shekara ta 1978, an yi sauye-sauye sosai a fannoni daban daban na zamantakewar al'ummar kabilar Korea, kuma zaman 'yan kabilar ya samu kyautatuwa kwarai da gaske.
Kabilar Korea tana da al'adun gargajiya iri daban daban, 'yan kabilar su gwanaye ne wajen waka da rawa. A lokacin salla da hutu, suna son nuna kaunarsu ta waka da rawa.
Haka kuma wasannin motsa jiki na kabilar Korea suna da halin musamman. Wasan kokawa wasa ne da suke so tun fil azal. Ban da wannan kuma maza na kabilar suna son kwallon kafa sosai.
Game da sha'anin ilmi, 'yan kabilar Korea suna mai da hankali sosai kan aikin koyarwa. A farkon shekaru 30 na karni na 20, sun kafa makarantu da dama. Kamar yadda 'yan kabilar su kan ce, gwamma mu ci fatar itatuwa maimakon mu hana yaranmu shiga makaranta.(Kande)
|