Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-14 17:41:52    
Mataimakin wakilin kasar Sin a M.D.D. ya bayyana yadda kasar Sin take goyon bayan bunkasuwar kasashen Afirka

cri
A ran 13 ga wata, lokacin da Liu Zhengmin, mataimakin wakilin kasar Sin a M.D.D. yake jawabi a gun taro game da sabuwar dangantakar abokanataka ta Afirka da aka yi bisa manyan tsare-tsara a M.D.D., ya bayyana yadda kasar Sin ke goyon bayan kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa.

Mr. Liu ya ce, tun daga shekarar 2000, gwamnatin kasar Sin ta riga ta soke basusuka 156 da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 10.5 da kasashen Afirka 31 wadanda suka ci basusuka sosai ko suke fama da talauci kwarai suka ci. A waje daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta dauki hakikanan matakai, wato ta bai wa kasashen Afirka matsayin ba da fifikon ciniki. Bugu da kari kuma, tun daga shekarar da muke ciki, kasar Sin ta fara daina buga harajin kwastam ga wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Afirka 25 wadanda suka fi talauta.

A sa'in daya kuma, Mr, Liu ya ce, yin hadin guiwa a fannin raya albarkatun kwadago tana daya daga cikin muhimman fannonin yin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. A shekarar bara, kasar Sin ta gayyaci mutane fiye da dubu 3 na kasashe da kungiyoyi 50 na Afirka da suka zo kasar Sin domin samun horarwa. Yanzu, dalibai kusan dubu 1 da dari 1 na kasashen Afirka 46 suna yin amfani da kudin kyauta da gwamnatin kasar Sin ke samar musu domin yin karatu a kasar Sin. (Sanusi Chen)