Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-13 17:27:23    
Masana'antun kasar Sin ke kokarin fitar da shahararrun samfur na kayayyakinsu

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kayayyaki, kirar kasar Sin sun sami karbuwa sosai a kasuwannin kasashe daban daban. A lokacin da ake sayar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje, sannu a hankali masu aikin masana'antu na kasar na zamani sun kara fadakar da kansu dangane da muhimmancin samfur na kayayyakinsu ga bukasa masana'antunsu. Yanzu, ana ta fitar da shahararrun samfur na kayayyaki da yawa irin na zamani.

A da, yawancin samfur na motoci da aka sayar a kasar Sin na kasashen waje ne. Amma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, masana'antun kasar Sin sun sha fitar da shahararrun samfur na motocinsu, wadanda suka hada da "Chery" da "Xiali" da sauransu. Alal misali, ba ma kawai motoci masu samfur "Chery" da masana'antun kera motoci na kasar Sin ke fitarwa suna samun karbuwa sosai daga wajen masaya na kasar ba, har ma ana fitar da su zuwa kasashen waje. A farkon rabin shekarar nan, kasar Sin ta fitar da motoci masu samfur "Chery" zuwa kasashe da yankuna wadanda yawansu ya wuce 40. Ka zalika kasar Sin ta riga ta fara sayar da injunan motoci masu samfar "Chery" a kasuwannin kasashen arewacin Amurka, yawan irin wadannan injuna da kasar Sin ta fitar zuwa kasar Amurka ya wuce 7000 a farkon rabin shekarar nan.

Ban da motoci kuma, kasar Sin tana fitar da shahararrun samfur na kayayyakin zamani. An kafa babban kamfanin kera kayayyakin digital mai suna "Huaqi" na birnin Beijing ne a shekarar 1993. Yanzu, kayayyakin zamani iri daban daban kamar kyamarar digital da sauransu da kamfanin ke fitarwa suna samun karbuwa sosai daga wajen masaya na kasar Sin. Malam Feng Jun, babban direkta na kamfanin ya bayyana cewa, "mun fahimci sosai cewa, samun shahararrun samfur na kayayyaki na kasarmu yana da matukar muhimmanci. Amma babu yadda za a yi a mayar da samfur na kayayyaki da su zama shahararrun samfur na kayayyaki a duniya, sai da farko dai an mayar da su da su zama shahararrun samfur na kayayyaki a kasarsu. Mun hakake bisa kokarin da ake yi, za a sami shahararrun samfur na kayayyaki da yawa a kasar Sin mai yawan mutane miliyan 1300."

An kafa babban kamfanin fasahar Internet mai suna "Baidu" na kasar Sin ne a shekarar 2000. A farkon lokacin kafuwarsa, babban aikinsa shi ne samar da fasaha ga manyan tashoshin Internet. Bayan shekara 1 da aka kafa ta, sai Malam Li Yanhong wanda ya kafa babban kamfanin nan ya yanke shawara a kan kafa tashar musamman ta samun adireshin shafin internet mai suna "Baidu". A shekarar 2005, kamfaninsa ya fara sayar da takardun hannun jarinsa a kasuwar hada-hadar kudi ta NASDAQ ta kasar Amurka. Malam Li Yanhong ya ce, "yayin da masu zuba jari suka amince da kamfaninsa, to, samfur na kamfaninsa sai kara zama shahararren samfur yake yi. Muna fatan nan da wani tsawon lokaci, sannu a hankali masu zuba jari za su gane cewa, kasar Sin za ta iya fitar da samfur na kayayyakinta da yawa a kasar Sin."

Yanzu, kamfanoni da yawa suna ta kashe makudan kudade wajen fitar da shahararrun samfur na kayayyakinsu. Da Malam Bu Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa, "yanzu, kayayyaki kirar kasar Sin sun shahara sosai a ko ina cikin duniya. Amma ya kamata, mu yi kayayyaki da ake kirkirowa a kasar Sin, wato mu mayar da kayayyaki, kirar kasar Sin don su zama kayayyaki da ake kirkirowa a kasar Sin, ka zalika mu sami shahararrun samfur na kayayyakinmu. " (Halilu)