Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-13 17:25:05    
Gwamnatin birnin Shanghai na himmantuwa wajen yin wani dan wasan motsa jiki domin taron wasannin Olympic na Beijing

cri
An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan tseren fitattun direbobin motoci na ' Formula-1' na shekarar 2006 a birnin Shanghai na kasar Sin. Wannan dai yana daya daga cikin gasannin motsa jiki iri daban daban dake bisa matsayi mafi gwaninta tsakanin 'yan wasa na kasa da kasa da gwamnatin birnin Shanghai ta shirya a shekarar da muke ciki. Birnin Shanghai, shi ma wani wuri ne inda za a gudanar da wassu gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Gwamnatin birnin Shanghai tana nan tana yin amfani da zarafin shirya wadannan gagaruman gasanni tsakanin 'yan wasa na kasa da kasa domin daukaka ci gaban ayyukan share fage ga gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na shekarar 2008 daga dukkan fannoni.

Birnin Shanghai yana daya daga cikin rassan wurare, inda za a gudanar da gasar kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing. Bisa ajandar gasanni da aka tsara, an ce, za a shirya gasanni 9 na mataki na farko na wasan kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing tun daga ran 6 zuwa ran 15 ga watan Agusta na shekarar 2008 a birnin Shanghai. A wannan shekara, gwamnatin birnin Shanghai ta riga ta dauki nauyin bakuncin shirya gasar fid da gwani ta wasan iyo na gajeren zango na duniya a shekarar 2006, da gagarumar gasar ba da kyautar zinariya ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Shanghai na hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasa da kasa a shekarar 2006 da kuma gasar fid da gwani ta bada babbar kyauta ta kasar Sin ta wasan tseren fitattun direbobin motoci na ' Formula-1' na duniya da dai sauran muhimman gasanni na kasa da kasa daya bayan daya; Ban da wannan kuma, a watan Nuwamba na wannan shekara, gwamnatin birnin Shanghai za ta shirya gasar karshe ta cin kofin Master na wasan tennis a shekarar 2006. Mr. Qiu Weichang, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta birnin Shanghai ya yi hasashen, cewa gwamnatin birnin tana matukar kokari wajen shirya wassu gagaruman gasanni dake bisa matsayi mafi gwaninta tsakanin kasa da kasa, wannan dai zai ba da amfani ga gwamnatin birnin wajen shire fage ga gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing.

Mr. Qiu ya kuma kara da, cewa wadannan gasanni sun kasance tamkar wani kyakkyawan dandali wanda za mu yi amfani da shi wajen gudanar da harkokin shirye-shiryen gasanni a nan gaba da kuma yin cudanya tsakanin kungiyoyin kasashen duniya da na wasannin motsa jiki na kasar Sin. Yanzu muna yin namijin kokari wajen gudanar da ayyuka iri daban daban da kyau na shirye-shirye da share fage ga gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na shekarar 2008.

A farkon wannan shekara, gwamnatin birnin Shanghai ta fito da ra'ayin cewa, kamata ya yi dukkan mazauna birnin su yi farfaganda da kuma yin hidima ga taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Manufar ayyukan share fage da gwamnatin birnin Shanghai take yi, ita ce 'Yin hidima ga taron wasannin Olympic na Beijing'. Ban da wannan kuma, sau da yawa ne wassu jami'an da abun ya shafa na birnin suka halarci tarurrukan kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da na kwamitin sulhu na taron wasannin Olympic na 29 na kwamitin wasannin Olymmic na kasa da kasa; Kazalika, sassan da abun ya shafa na birnin Shanghai sun gayyaci wassu mahukuntan kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing don su ba da jaroganci da kuma shiga harkokin gudanar da gagaruman gasanni iri daban daban na duniya da aka yi a birnin na Shanghai. Ko shakka babu, ta hakan, gwamnatin birnin Shanghai ta samu dimbin fasahohi da kuma kwararrun mutane a fannin shirya gasanni, da raya harkokin kasuwanci, da sayar da tikitoci, da karbar 'yan jarida da kuma na daukar mutane masu aikin sa kai da dai sauran fannoni.

Jama'a mau saurare, gwamnatin birnin Shanghai ta kuma dauki nauyin shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa na mata a shekara mai zuwa. Lallai wannan ya samar da wata kyakkyawar dama ga gwamnatin birnin Shanghai wajen yin gwajin aikin share fage ga gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing.. ( Sani Wang )