Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-13 12:38:51    
Takardar bayani kan ' harkokin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin na shekarar 2006'

cri

A ran 12 ga watan da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata takardar bayani kan ' harkokin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin na shekarar 2006'. Takardar bayanin ta ce, nan da shekaru biyar masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta gaggauta yunkurin samun bunkasuwa a fannin fasahohi da na kimiyya na zirga-zirgar sararin samaniya da kuma sauran fannoni yayin da take ingiza hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarori biyu da kuma bangarori da dama.

A gun taron ganawa da 'yan jarida da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shrya a ran 12 ga wata, Mr. Sun Laiyan, shugaban hukumar kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin ya yi bayani kan wannan takarda. Ya furta, cewa yanzu kasar Sin ta riga ta zama kasa ta uku a duniya dake nazarin ayyukan harba kumbo mai daukar mutane zuwa sararin samaniya ita kanta ; Ban da wannan kuma, a karo na farko ne kasar Sin ta gudanar da harkar gwaje-gwaje tare da halarar mutane a sararin samaniya da kuma yin binciken wata. Nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya bisa wannan tushe. Mr. Sun ya fadi, cewa : ' Nan da shekaru biyar masu zuwa ko dan tsawon lokaci kadan, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane da kuma Carrier Rocket na sabon salo zuwa sararin samaniya, da kuma cikakken tsarin sadarwa da na watsa shirye-shirye ta hanyar taurarin watan dan adam'.

Domin cimma wannan manufa, gwamnatin kasar Sin za ta bayar da fifiko ga goyon bayan harkar bunkasa fasahohin kera watan dan adam fiye da komai ; Sa'anan za ta yalwata harkar harba kumbuna masu dauke da mutane zuwa sararin samaniya kamar yadda ya kamata da kuma sa kaimi ga kafa tsarin zuba jari a fannin zirga-zirgar sararin samaniya ta hanyoyi da dama, ta yadda za a gaggauta kafa babban kamfanin zamani na zirga-zirgar sararin samaniya a duniya.

Jama'a masu saurare, kuna sane da, cewa mata muhimmiyar manufar bunkasa sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya da gwamnatin kasar Sin take yi, ita ce yin hidima ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa. Yanzu, kasar Sin na yin hadin gwiwa sosai tare da hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta Turai. Yin haka, ya kawo moriya mai tsoka ga bangarorin biyu a fannin sha'anin noma, da yanayin sama da kuma na rage yawan afkuwar bala'i daga indallahi da dai sauran fannoni. Nan gaba ma, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza yunkurin bunkasa sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya don daukaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar. Mr. Sun Laiyan ya futa, cewa :'Kasar Sin wata kasa ce mai tasowa. Manufar bunkasa sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya da gwamnatin kasar Sin take yi, ita ce yin hidima ga raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa ,da kuma daga matsayin kasarmu a duniya a fannin bunkasa kimiyya da fasaha. Muna ganin, cewa yalwata sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya zai iya taimaka wajen magance dimbin matsaloli da muke fuskanta a fannin tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa'.

Dadin dadawa, Mr. Sun Laiyan ya karfafa magana, cewa gwamnatin kasar Sin za ta kara yin hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe a fannin sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya. Ya fadi, cewa :

'Karni na 21, sabon karni ne na yin bincike da kuma yin amfani da sararin samaniya da bil adama ke yi. Kara yin musanye-musanye da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, wata kyakkyawar hanya ce da kasashen duniya suke bi wajen bunkasa sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya. Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga yin haka bisa ka'idar samun moriya da juna bisa matsayin daidaici, da yin amfani da fasahohi a fannin zirga-zirgar sararin samaniya cikin lumana da kuma samun bunkasuwa tare'. ( Sani Wang )