Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-12 18:36:47    
Hadin guiwa a tsakanin Sin da Afirka tana dogara kan tarihin aminci a tsakaninsu

cri
"Dangantakar sada zumunta sosai a tsakanin Sin da Afirka tana dogara kan dogon tarihin aminci da ke kasancewa a tsakaninsu. Ba kamar kasashen yammacin duniya suke fadi cewa, wai kasar Sin ta raya dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka ne domin mallaka da yin amfani da albarkatun halittu na Afirka." Shehun malami Malarica ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xin Hua na kasar Sin kafin a kaddamar da taron tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing.

Mr. Malarica, wani sanannen shehun malami ne da ke nazarin zaman al'umma a kasar Zimbabwei. Ya dade yana kulawa da yin nazari kan cigaban dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya ce, kasar Sin aminiya ce ta nahiyar Afirka a cikin tarihi. Sabo da haka, duk abubuwan da aka samu yanzu sakamako ne domin bunkasuwar irin wannan dangantakar sada zumunta a tsakaninsu. A da, kasar Sin da kasashen Afirka su kan bayyana zumuncinsu kan harkokin siyasa, amma yanzu, kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu suna yin gyare-gyare kan tattalin arzikinsu, an kirkiro damar yin hadin guiwa masu dimbin yawa a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Sabo da haka, ko shakka babu, suna bayyana zumunci ne a fannin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya.

Sa'an nan kuma, dole ne a duba matsaloli ta fuskar tarihi, don haka, za a iya fahimtar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. An haifar da irin wannan dangantaka ne cikin dogon lokacin da ya wuce kafin ko bayan da kasashen Afirka suka samu 'yancin kai.

Shehun malami Malarica ya ce, jama'ar yawancin kasashen Afirka sun samu taimakon kudi daga kasar Sin da sauran kasashen duniya wadanda suka nuna musu tausayi lokacin da suke yin gwagwarmaya kan mulkin mallaka na yammacin duniya. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta kafa wa kasashen Afirka kyakkyawan muhalli a M.D.D. Kasashen Afirka ma suna nuna wa kasar Sin goyon baya a M.D.D. Bugu da kari kuma, kasar Sin ta ki yarda yammacin kasashen duniya su danne kasashen Afirka. Sakamakon haka, kasashen yammacin duniya sun haifar da wasu munanan tunani kamar shi "kasar Sin tana mulkin mallaka a Afirka".

"Wannan tsabar kishi ne", Mr. Malarica ya ce, "Kasashen yammacin duniya sun sace abubuwa da kayayyaki daga Afirka ta hanyoyin mulkin mallaka da fitar da tunaninsu na shimfida dimokuradiyyarsu a Afirka. Amma kasar Sin tana raya dangantakar hadin guiwar tattalin arziki irin ta moriyar juna a tsakaninta da kasashen Afirka. Haka nan kuma, kasar Sin ta kan raya dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka a matsayin abokiyar yin hadin guiwa. Amma kasashen yammacin duniya su kan sa idanunsu kan albarkatun halittu na Afirka."

"Wannan wasannin siyasa da na tattalin arziki ne da kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin, dole ne kasashen Afirka sun san wannan wasa, kada kasashen yammacin duniya su ci nasarar wasanninsu.", a cewar shehun malami Malarica.

Sa'an nan kuma, hakikanan abubuwa sun shaida cewa, dalilin da ya sa kasar Sin take jawo hankulan kasashen Afirka shi ne kasar Sin ta nuna wa kasashen Afirka aminci. Kuma tana son kulla wata sabuwar dangantakar hadin guiwa a tsakaninta da kasashen Afirka ta hanyar zuba jari a kan wasu masana'antun Afirka, amma kasashen yammacin duniya ba su so su yi haka. Suna neman cikakken ikon mallakar dukkan dukiyoyin masana'antu a Afirka. Hanyar dogo da ke tsakanin kasashen Tanzania da Zambia wani kyakkyawan misali ne. Wannan ayyuka ya iya tabbatar da cewa an riga an kafa wata sabuwar dangantakar hadin guiwar tattalin arziki mai kyau a tsakanin Sin da Afirka. Amma, har abada kasashen yammacin duniya ba za su yi haka ba.

"Abin da mutum ya shuka shi zai girba", in ji Malarica, dalilin da ya sa kasar Sin ta iya samun jerin kwangiloli daga kasashen Afirka shi ne, dangantakar hadin guiwa irin ta sada zumunta da ke tsakaninsu tana ta samun cigaba a cikin dogon lokacin da ya shige. (Sanusi Chen)