A kowace shekara , ran 15 ga watan Agusta na kalandar kasar Sin ranar bikin tsakiyar yanayin Kaka ce ta gargajiyar kasar Sin, wato da turanci ake cewa the Mid-Autumn Festival . Saboda wannan lokaci yana cikin tsakiyar yanayin A cikin shekaru 2000 da suka shige , bikin tsakiyar yanayin kaka kullum ya zama wani kyakkyawan biki ne ga kabilu daban daban na kasar Sin wajen kyautata lafiyar jiki da yin rigakafi da warkar da cututuka da kawar da abubuwa masu dafi .
Ana kasancewa da bayanoni da yawa wadanda suka sha bambam game da mafarin Bikin tsakiyar yanayin kaka . Wasu sun bayyana cewa , Bikin tsakiyar yanayin kaka ya faru ne daga al'adar lokacin rani ta zamanin da , wasu kuma suna ganin cewa , ya faru ne saboda girmamawar da mutanen dake zama a gabobin Kogin Yangtse na zamanin da ke nuna wa Dragen , wato dodon kasar Sin . Amma duk da haka galiban mutanen kasar Sin suna ganin cewa , ana yin bikin tsakiyar yanayin kaka ne musamman domin tunawa da mai dafa waina tamkar wata .
Sunan mai dafa waina tamkar wata shi ne Fu Shi . Ya yi zaman rayuwa ne a 'karni na 2 na kafin haihuwar Annabi Isa Alaihi Sallam a kasar Chin na lokacin yake-yaken Sarakuna na Zhanguo , bayan da wata kasar abokan gaba ta mamaye kasar mahaifarsa , ya ji haushi sosai har ya gudu zuwa kan babban tudu . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan wainar kasar Sin da Fu Shi ya dafa a kolin babban tudun . Bisa labarin da aka ruwaito mana cewa , tsohon bayani ya ce , Kwanan baya gwamnatin kasar Chin ta kira wani taron aiki kan yadda za a yi tsimin abinci , ciki har da shinkafa da masar da alkama da gero da dankali da saurasu .
Ranar da Fu Shi ya hawa kan tudun , ran 15 ga watan Agusta ce ta kalandar gargajiyar kasar Sin . Sabo da Fu Shi ya ji haushi kwarai da gaske kuma kwana biyu bai ci kome ba , shi ya sa ya gauraya kayayyakin lambu daban daban kuma ya dafa su har suka nuna . Bayan da suka yi sanyi , sai ya sa cikin fulawar alkama ya sake dafawa . Daga bisani dai ya zama abinci mai dadi kwarai da gaske kuma sifar waina tamkar karamin wata .
Li Bai , mawaki mai kishin kasa na Daular Tang ya taba rubuta wata waka cewa , A gaban gado yana kasance da hasken wata , Ina shakkar cewa shi ne kankara . Na daga kaina don ganin wata mai haske , sai na tuna da mahaifina .
Daga baya kuma , a wannan rana ta kowace shekara , domin tunawa da halin kirki na Li Bai , mutane su kan rataye jakunkuna masu kamshi, da cin wani abinci da ake kira Yuebing wato wainar tamkar wata . An riga an shafe shekaru fiye da dubu 2 ana yin irin wannan bikin tsakiyar yanayin kaka .
A cikin shekaru 2000 da suka shige , halin kirki na kishin kasa na shahararren mawaki Li Bai ya burge mutane sosai. Mutanen kasar Sin suna cin abinci mai sunan wainar tamkar wata a ranar bikin tsakiyar yanayin kaka ne musamman domin tunawa da Li Bai , har ya zama wani bikin duk al'umman kasar Sin .
Mr. Yang mingsheng , shugaban Kungiyar nazarin al'adun gargajiyar kasar Sin ya ce , ban da abinci wainar wata kuma , yana kasance da al'adar jama'a ta yin ado masu halin musamman a gun bikin tsakiyar yanayin kaka . A wannan rana , kowane iyali ya kan rataya wani zagayayyen madubi da ake kira mid-autumn mirror a bakin kofarsa domin yin rigakafi da kawar da ciwace-ciwace. Kuma akan yi gagaruman bukukuwan tsare-tsare da kwale-kwale a bakin kogi ko tafki a karkashin hasken wata , kuma an buga ganguna da kuge da yin kirarin farin ciki a kan kwale-kwale . (Ado).
|