Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 18:38:02    
Dabbobin da Sinawa ke yin amfani da su a wajen kirga shekaru

cri
Tambayar da za mu amsa a yau ta fito ne daga hannun malam Lawal Garba, mazauni Zuru, jihar Kebbi ta kasar Nijeriya. A cikin wasikar Email da ya aiko mana, ya ce, me ya sa Sinawa suna amfani da sunayen dabbobi a wurin kirga watanni na shekara. To, malam Lawal, Sinawa suna amfani da sunayen dabbobi ne a wajen kirga shekaru, ba wai wajen kirga watanni na shekara ba. Kirga shekaru da sunayen dabbobi al'adar gargajiya ce ta kasar Sin, wadda ta jawo sha'awa kwarai daga jama'ar kasashen waje, to, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari in bayyana muku wannan al'adar kasar Sin da ke da daddaden tarihi.

Masu sauraro, shekarar da muke ciki, wato 2006, shekara ce ta kare, kuma dukan yaran da aka haife su a shekarar, a kan ce, kare ne zai alamanta shekarunsu na haihuwa.

Dabbobi 12 ne ake amfani da su a wajen kirga shekara a kasar Sin, wato su ne bera da saniya da damisa da zomo da dragon da maciji da doki da rago da biri da kaji da kare da kuma alade. Game da asalin wannan hanyar da ake bi ta kirga shekaru da sunayen dabbobi, akwai bayanai da yawa. Wasu sun ce, shi sakamako ne da aka samu daga wajen hada hanyar da al'ummar kasar Sin ta zamanin da ke bi wajen kirga shekaru da kuma hanyar da kananan kabilun kasar suke bi ta yin amfani da sunayen dabbobi wajen kirga shekaru. Wasu kuma suna ganin cewa, an shigo da shi ne daga kasar Indiya. A kalla dai, jama'ar kasar Sin sun soma kirga lokatu na duk yini ne daga zamanin daular Han, wato a karni na uku kafin haihuwar Annabi Isa, (A.S), kuma A lokacin, akwai wani babban malami mai suna Wangchong, wanda ya yi bayani a kan dabbobin nan 12 da ake amfani da su a wajen kirga lokatai. Game da yadda aka zabi dabbobin nan da kuma jera su, akwai wani bayani na nuni da cewa, an zabi wadannan dabbobi da kuma yi musu layi ne bisa ka'idojin aikace-aikacensu a kowace rana. An ce, daga karfe 11 na dare zuwa karfe daya na asuba, lokaci ne da beraye ke fitowa fili sosai, shi ya sa an jera su a matsayi na farko. Sa'an nan, ta wannan hanyar ne aka jera sauran dabbobi, misali, daga karfe 7 zuwa karfe 9 na dare, kare ya kan soma aikinsa na tsaro, shi ya sa an jera shi a matsayi na 11. Daga baya, an kuma dauki dabarar nan a wajen kirga shekaru, kuma ana zagaya duk dabbobin sau daya cikin shekaru 12.

Akwai tatsuniyoyi da almara da dama a nan kasar Sin dangane da dabbobin da ake amfani da su a wajen kirga shekaru. Daga cikinsu kuma, akwai wata dangane da bera. Watakila ka ce, a cikin duk dabbobin nan 12, me ya sa aka jera bera a matsayi na farko? Ga shi bera, karami ne, har ma ya fi karanta a cikin dukan dabbobin nan 12. Ga kuma karfinsa, bai fi saniya da damisa da dragon da kuma doki ba. Amma ko kuma yana da hali nagari? A'a, ba kamar yadda saniya ke tsayawa kan akidarta ba, kuma ba shi da halin kirki na zomo da kuzari na doki da kuma biyayya ta rago. A kan maganar hikima kuma, biri da kare duk sun fi shi. To, shi ke nan, me ya sa aka sa shi a matsayi na farko? Yanzu ga ta nan tatsuniyar, don ku sami amsar.

An ce, bayan da bera da dai sauran dabbobi suka ci zaben zama dabbobin da za a yi amfani da su a wajen kirga shekaru, sai bera ya ce, 'ya kamata a sanya ni a matsayi na farko.' amma saniya da doki da kuma rago ba su yarda ba, sun ce, 'me ya sa ya kamata ka zo na farko?' Bera ya amsa cewa, 'sabo da na fi girma'. Sai saniya da doki da rago suka barke da dariya, sun ce, 'ko har ka fi mu girma?' Bera ya ce, 'ba wai mu ne muke iya yanke hukunci ba. Bari mu ji me jama'a za su fada.' Saniya da doki da rago sun yarda. Sabo da haka, saniya ta shugabanci doki da rago da kuma bera su yi yawo a kan titi bi da bi, don su ji me jama'a za su fada.

A kan titi, ganin saniya, jama'a sun ce, 'wannan saniya tana da karfi.' Sa'an nan doki ya zo, jama'a sun ce, 'Mmm, wannan doki yana da tsayi.' Da suka ga rago, sun ce, 'ragon yana da kiba'. Ga shi bera yana yawo a karshe, fitowar wannan babban bera ba zato ba tsammani, sai jama'a sun yi kira, 'Kash, ga bera mai girman haka, ga bera mai girman haka!' Sabo da haka, ba yadda aka yi, sai aka sanya bera a matsayi na farko.(Lubabtu)