A gun bikin sinima na 63 na Venice da aka rufe a kwanan nan ba da dadewa ba, saurayi direktan sinima na kasar Sin Jia Zhangke ya sami babbar lambar yabo mai suna "Zakin zinariya" bisa sunan sinima mai kyau sosai da ke da lakabi haka: Mutum mai kirki na Sanxia, saboda haka ya zama direktan sinima na 5 na sinawan da ya samun irin lambar nan , kuma lambar yabo ce da wani mutumi mai daukar sinima na babban yankin kasar Sin ya samu bayan da Mr Zhang Yimo ya sami irin wannan lambar a shekarar 1999.
Sinimar da ke da lakabin " Mutum mai kirki na Sanxia" tana kunshe da labaran soyayya guda biyu. An sami labaran a wani karamin garin da ke bakin ayyukan ruwan Sanxia wadanda ake gina su yanzu a kasar Sin. Maza biyu da mata biyu sun shiga soyayya ko sun yi rabuwar aurensu bisa fahimtar juna sosai da sosai, a kan hanyarsu ta neman soyayyar gaskiya, dukansu sun sami sakamako mai kyau wajen zaman rayuwa. Shugaban kwamitin ba da kimantawa ga sinima na bikin nan kuma mashahurin direktan sinima na kasar Faransa Catherine Deneuve ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya bayan bikin bayar da lambobin yabo cewa, bayan da mambobin ba da kimantawa kan sinima na wannan bikin suka kallisinimar nan, sai suka ji mamaki sosai, hotunan sinimar da aka dauka na da kyaun gani sosai, kuma labaran da ke cikinta sun ba da sha'awa sosai, ta burge wa 'yan kallo sosai da sosai, sinimar ita ce ta ke da halayen musamman sosai da sosai.
An haifi Jia Zhangke a gundumar Fenyang ta lardin Shan'xi a shekarar 1970, wato yanzu yana da shekaru 36 da haihuwa. Mahaifinsa shi ne wani malamin makarantar sakandare, mahaifiyarsa ita ce akawun kanti. A shekarar 1993, Jia Zhangke ya soma karatu a jami'ar koyar da ilmin sinima ta birnin Beijing, bayan shekaru uku da suka wuce, sai ya soma aikin daukar sinima shi kansa. Ya zuwa yanzu, yawan sinima da Jia zhangke ya dauka ya kai 5.
Daga karamin gari zuwa babban birni, wato Beijing, Mr Jia Zhangke ya ji bai dace sosai ba, ya bayyana cewa, bayan da aka kara girman birane, musamman ma bayan da birnin Beijing ya sami damar shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008, sai mutane da yawa suka tinkaro suka shiga cikin birnin, ni ma na sauko nan birnin Beijing a shekarar 1993 daga gundumar Fenyang na lardin Shan'axi , wato wani karamin gari, sanimar da ke da lakabin " Mutum mai kirki na Sanxia" ta bayyana yadda wasu samari da suke samun aikin yi a birane kuma suke gamu da matsaloli da matsi da abubuwa masu bacin rai da neman fatansu da dai sauransu.
Mr Jia Zhangke ya kara da cewa, ina son bayyana abubuwan gaskiya sosai , shi ya sa ina fatan sinimar da na dauka ta iya bayyana halin da ake ciki yadda ya kamata, wato 'yan wasa sun nuna wasanni ba bisa kayantarwa ba, shi ya sa na nemi wadanda ba 'yan wasa na gaskiya ba da su nuna wasanni, ina son su nuna wasanni a daidai yadda halin da ake ciki .
A lokacin da Jia Zhangke yake daukar sinimar da ke bayyana abubuwan gaskiya, sai ya ji cewa, wasu mutane ba su so su bayyana abubuwan da ke da nasaba da su ba, amma wannan ya kara jawo sha'awarsa, shi ya sa ya tsai da kudurin daukar sinimar da ke bayyana labarai don bayyana wadannan abubuwan da suke kasancewa.
Ana son kiransa da cewar wai direktan sinima na zuri'a ta 6 ta kasar Sin, lokacin da ya soma daukar sinima, lokaci ne da sinimar kasar Sin suke neman shiga kasuwanni, a wani fanni, yana son nacewa ga bin ra'ayinsa na bayyana fasahohin wasanni, amma a sa'I daya kuma, yana fuskantar kalubalen samun kudade, kullum Mr Jia Zhangke ya nace ga bin hanyar daukar sinima don fuskantar hakikanan abubuwan da ke kasancewa a kasar Sin da kuma bayyana abubuwan da rukunonin mutanen da ke matsayin kasa na kasar Sin suka ji, amma abin da ya dauka na da halayen musamman sosai.(Halima)
|