Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 09:03:42    
Kasar Sin ta kara karfafa aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba a birnin Beijing,hedkwatar kasar Sin,babbar hukuma mai kula da aikin wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta shirya wani taron manema labarai inda aka yi bayani kan sakamakon da aka samu bayan da aka yi karo na biyu na aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa.A kwana a tashi,kasar Sin ta kara mai da hankali kan wannan aiki saboda aikin yana da muhimmanci sosai.A cikin shirin na yau,za mu yi muku bayani kan wannan.

Dalilin da ya sa aka yi aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa shi ne domin kara sanin halin jikin da mutanen kasa ke ciki,alal misali,siffar jiki da amfanin jiki da ingancin jiki da sauransu,wato an zabi wasu daga cikin dukkan mutanen kasa,an yi jarrabawa kan jikinsu,daga baya kuma an yi nazari kan sakamakon da aka samu.A kullum,kasashe masu ci gaba da yawan gaske suna mai da hankali sosai kan wannan,alal misali,a kasar Japan,an riga an gudanar da wannan aiki fiye da shekaru dari daya,kuma za a sanar da sakamakon da aka samu cikin lokacin da aka tsara.Bisa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al`ummar kasa,gwamnatin kasar Sin ta kara mai da hankali kan ingancin lafiyar jikin mutanen kasa.Ya zuwa shekara ta 2000,kasar Sin ta fara aikin nan,kuma an tanadi cewa,za a yinsa sau daya a duk shekaru biyar.Game da wannan,mataimakiyar shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin madam Hu Jiayan tana ganin cewa,aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa da aka yi a shekara ta 2000 ya sa harsashe mai kyau ga aikin binciken halin lafiyar jikin mutanen kasa.Ta ce: `A shekara ta 2000,sassan da abin ya shafa guda 9 na kasar Sin sun tsara tsarin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa a jihohi da birane da yawansu sun kai 31 a duk fadin kasar,kuma sun tattara takardun bayani da yawa.`

A shekara ta 2005,babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin da ma`aikatar kula da aikin ba da ilmi ta kasar Sin da ma`aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin da sauran sassa bakwai sun yi karo na biyu na aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa a jihohi da birane 31 na kasar Sin,kuma sun kammala aikin kafin karshen shekara ta 2005.A gun aikin da aka yi,an zabi `yan kasar Sin wadanda shekarunsu da haihuwa daga 3 zuwa 69 guda dubu dari biyu da ashirin da uku da dari biyu,daga baya kuma an yi musu bincike da kuma jarrabawa daga duk fannoni,a karshe dai an sami cikakken sakamako.

Abu mafi muhimamnci shi ne bisa karo na farko an fara yin amfani da fihirisa wato index yayin da ake gudanar da aikin nan,madam Hu Jiayan ta ce, `Tun daga shekara ta 2000,mun fara yin nazari kan hadadden fihirisa na ingancin lafiyar jikin mutanen kasa don nunawa sauye-sauyen matsayin ingancin lafiyar jikin mutanen kasa,daga baya kuma za a tsara shirin motsa jiki mai dacewa don kyautata ingancin lafiyar jikin mutanen kasa.`

A gun taron watsa labaran da aka yi,shugaban ofishin kula da aikin motsa jiki na jama`a na babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin Sheng Zhiguo ya yi bayani kan sakamakon da aka samu daga karo na biyu na aikin binciken ingancin lafiyar jikin mutanen kasa,ya ce,ana iya cewa,matsayin ingancin lafiyar jikin mutanen kasar Sin ya dada ingantuwa kadan in an kwatanta shi da na shekara ta 2000,kuma yawan maza masu fama da ciwon kiba da ya yi fiye da kima sun karu a bayyane,ban da wannan kuma,ingancin lafiyar jikin mazaunan birane ya fi na mazaunan kauyuka,a karshe dai,an gano cewa,ingancin lafiyar jikin mutanen shiyyar dake gabashin kasar Sin ya fi na yammacin kasar.

Mataimakiyar shugaban babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin madam Hu Jiayan ta bayyana cewa,dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta yi kokari kan wannan aiki shi ne domin kara sanin sauye-sauyen halin ingancin lafiyar jikin mutanen kasa,haka kuma za a ba da taimako ga mutanen kasa domin kyautata lafiyar jikinsu.Madam Hu Jiayan ta ce: `Hukumomin gwamnatin da abin ya shafa kamarsu hukumar kula da wasannin motsa jiki da ta kula da harkokin jama`a da ta kwadago da ta ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a da sauransu za su gama kansu domin kafa wani tsarin ba da hidima ga lafiyar jikin jama`a.` (Jamila Zhou)