Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 08:59:46    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(05/10-11/10)

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,jami`ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ci nasara kan aikin nazarin fasahar hana aukuwar gobara a cikin dakunan wasannin Olimpic,an yi wannan aiki ne musamman domin hana aukuwar gobara a cikin dakunan wasannin Olimpic.A halin da ake ciki yanzu,an riga an fara yin amfani da wannan fasaha a wasu dakunan wasannin Olimpic.

Ran 7 ga wata,an kammala gasar cin kofin duniya ta wasan takobi ta shekara ta 2006 wadda aka shafe kwanaki 9 ana yinta a birnin Turin na kasar Italiya,`dan wasa daga kasar Sin Wang Lei ya zama zakaran gasar takobi wato `epee`,wannan karo na farko ne da kasar Sin ta sami lambawan a cikin gasar takobin duniya,ban da wannan kuma kungiyar `yan wasan kasar Sin ta sami lambawan a cikin gasar takobi ta mata da aka yi tsakanin kungiya kungiya,wannan shi ma karo na farko ne da kungiyar kasar Sin ta zama zakaran gasar.

Daga ran 30 ga watan jiya zuwa ran 7 ga wata,an yi gasar cin kofin duniya ta wasan daukan nauyi ta shekara ta 2006 a birnin San Domingo na jamhuriyar kasar Dominica,gaba daya `yan wasa 569 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 79 sun shiga wannan gasa,a gun gasannin da aka yi,kungiyar kasar Sin ta samu babbar nasara,gaba daya ta sami lambobin zinariya 20 daga cikin 45,wato lambobin zinariya da ta samu sun fi yawa,kungiyar kasar Rasha ta zama lambatu.

Ran 8 ga wata,a birnin Doha na kasar Quatar,an yi bikin sa wuta kan wutar yula ta wasannin Asiya,a sa`i daya kuma,an yi gudun ba da wutar yula domin wannan.Mai jiran gadon sarrauta na kasar Quatar kuma shugaban kwamitin wasannin Olimpic na kasar Sheikh Tamim ya sa wuta kan wutar yula kuma ya sanar da cewa za a fara gudun ba da wutar yula.Za a yi kwanaki 55 ana yin aikin a kasashen Asiya 15,tsawon gudun zai kai kilomita dubu 50.Kuma za a yi taron wasannin Asiya na 15 a birnin Doha daga ran 1 zuwa ran 15 ga watan Disamba na wannan shekara.

Ran 7 ga wata,an kawo karshen karo na karshe na gasar cin kofin duniya ta wasan harbe-harbe ta shekara ta 2006 a birnin Granada na kasar Spain,a gun gasannin da aka yi,kungiyar `yan wasan kasar Rasha ta sami lambobin zinariya 9 da na azurfa 2 da na tagulla 4,kungiyar kasar Sin kuwa ta sami lambar zinariya daya da na azurfa 6 da na tagulla 3.(Jamila Zhou)