Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-10 20:17:21    
Kasar Madagascar ta dora muhimmanci kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri
A ran 9 ga wata, yayin da shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanana ke ganawa da Chen Jian, mai ba da taimako ga ministan kasuwanci na kasar Sin wanda ya kai wa kasar ziyara, ya bayyana cewa kasar Madagascar ta dora muhimmanci sosai kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Shi kansa zai jagoranci wata tawagar kasar don halartar taron, kuma ya yi imani cewa, tabbas ne taron zai samu nasara.

Haka kuma Mr. Ravalomanana ya bayyana cewa, yana mai da hankali sosai kan dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin kasashen Madagascar da Sin, kuma za a karfafa yin cudanyar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. A waje daya kuma ya roki Chen Jian da ya mika gaisuwarsa ga takwaransa na kasar Sin Hu Jintao, kuma yana jiran ganawa tsakaninsa da shugaba Hu a birnin Beijing.(Kande Gao)