Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-10 18:55:57    
Cin dafaffen tumatir zai iya shawo kan ciwace-ciwacen zuciya da hauhawar jini

cri
Tumatir wani irin kayan lambu ne da mutane suke son ci, amma yawancin mutane suna son cin tumatir ba tare da dafa shi ba. A cikin kwanakin nan, masu ilmin kimiyya na kasar Birtaniya sun gano cewa, tumatir da aka dafa shi zai fi ba da taimako ga lafiyar jikin mutane. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bayan da aka dafa tumatir, jikin mutane ya fi karbar wani irin abin gina lafiya da jiki da ke cikin tumatir wanda ake kiransa lycopene a turance da sauki, kuma wannan abin gina lafiyar jiki zai iya ba da taimako wajen shawo kan ciwace-ciwacen zuciya da hauhawar jini.

Idan kitsen da ke taruwa a jijiya ya yi yawa fiye da kima, to zai hana jini zagaye cikin jiki yadda ya kamata, ta haka zai haddasa ciwace-ciwacen zuciya da hauhawar jini.

Masu ilmin kimiyya na jami'ar Liverpool John Moores ta kasar Birtaniya suna gano cewa, a cikin tumatir, akwai wani abin gina lafiya da jiki da ake kiransa lycopene, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan toshewar hanyoyin jini. Haka kuma jikin mutane ya fi karbar lycopene daga dafaffen tumatir da sauki idan an kwatanta shi da tumatir wanda ba a dafa shi ba. Ban da wannan kuma wani mai ilmin kimiyya ya yi nuni da cewa, ya fi kyau a dafa tumatir tare da mai.

Ya zuwa yanzu, manazarta suna kimantawa dabaru iri daban daban na dafa tumatir domin tabbatar da cewa, ta wace hanya ce jikin mutane zai karbi lycopene mafi yawa.(Kande Gao)