Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-09 18:49:12    
Bayani game da kabilar Yi

cri
Kabilar Yi tana daya daga cikin kananan kabilun da suke da dogon tarihi da al'adun gargajiya sosai a nan kasar Sin. Yawancin mutanenta suna zama a larduna 3, wato Yunnan da Sichuan da Guizhou kuma da yankunan arewa maso yammacin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta. A lardin Sichuan, akwai shiyyar Liangshan ta kabilar Yi mai cin gashin kanta. A lardin Yunnan, akwai shiyyar Chuxiong ta kabilar Yi mai cin gashin kanta da shiyyar Honghe ta kabilun Hani da Yi mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar ya kai fiye da miliyan 7 da dubu dari 7. Suna da yare da kalmomin Yi.

A da, tattalin arzikin yankunan da mutanen kabilar Yi suke zama ya ja da baya kwarai. Yawancin mutanen kabilar sun yi sana'ar aikin gona, sun yi noman masara da alkama da wake da shimkafa da dai sauransu. Zaman rayuwar jama'ar kabilar Yi ba shi da kyau.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, jama'ar kabilar Yi sun yi kokari sun raya tattalin arziki da zaman al'ummarsu a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce. Yanzu, an riga an kafa masana'antun sarrafa bakin karfe da haka kwal da kamfanonin samar da wutar lantarki da yin takin zamani da kera injunan aikin gona kuma da yin abinci. Alal misali, a birnin Gejiu, inda mutanen kabilar Yi suke zama, akwai kamfanin sarrafa kuza da yake daya daga cikin muhimman kamfanonin nonferrous metal na kasar Sin. Yankin Liu Panshui na lardin Guizhou, inda mutanen kabilar Yi suke zama, akwai muhimmin kamfanin haka kwal. Bugu da kari kuma, hanyoyin dogo da hanyoyin motoci da suke ratsawa yankunan kabilar Yi sun kyautata halin yin sufurin da ake ciki a wadannan yankuna.

A cikin dogon tarihin da ya wuce, jama'ar kabilar Yi sun kirkiro al'adun gargajiya na kabilar da ke da launi iri iri. Ire-iren litattafan tarihi da na adadi da na addini na kabilar da aka rubuta su da hannu sun kai fiye da dubu 1. Yanzu an riga na juya su cikin harshen Sinanci kuma an yi dab'insu.

Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Yi suna da sha'awar wakoki da raye-raye.

Mutanen kabilar Yi sun fi son cin masara da alkama da shimkafa da wake kuma da naman shanu da na kaza.

Gidajen da mutanen kabilar Yi suke zama sun kama da na kabilar Han.

A yankunan kabilar Yi, iyaye sun fi son zama tare da auta. Namiji daya ya iya auren mace daya. Lokacin da ake yin aure, dole ne iyayen ango sun biya kudin aure ga iyayen amariya.

Mutanen kabilar yi suna da bukukuwa iri iri, ciki har da "Bikin Yola" da "Bikin sabuwar shekara ta kalandar kabilar Yi" da "Bikin raye-raye da waka". A cikin wadannan bukukuwa, Bikin Yola ya fi muhimmanci ga mutanen kabilar Yi.(Sanusi Chen)