Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-06 20:32:46    
Ana kara inganta hadin guiwar tattalin arziki a yankin mashigin teku na Bac Bo

cri

Mashigin teku na Bac Bo yanki ne da ke hada kasashen Sin da Vietnam, kuma yana fuskantar tsibirin Hainan na kasar Sin. Jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokin kanta wadda ke kuriyar mashigin teku na Bac Bo, tana daya daga cikin jihohin kasar Sin inda 'yan kananan kabilu da yawa ke zama. Ka zalika akwai kasashe guda 6 na kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya Wato ASEAN kamar Malasiya da Indonesiya da Brunei da sauransu wadanda ke zagayen jihar nan. A sakamakon ci gaba da ake ta samu wajen raya yankin cinikayya cikin 'yanci a tsakanin Sin da Kungiyar ASEAN, mashigin teku na Bac Bo ya fara jawo hankulan mutane sosai.

A kwanakin baya, an shirya taron dandalin tattaunawa na karo na farko a kan hadin kan tattalin arzikin yankunan mashigin teku na Bac Bo a birnin Nanning, fadar gwamnatin jihar Guangxi ta kasar Sin. Jami'an gwamnatoci da masanan ilmi da wakilan shahararrun masana'antu sama da 160 wadanda suka fito daga kasashen Brunei da Indonesiya da Malasiya da Sin sun halarci taron, inda suka yi tattaunawa mai zurfi a kan batun hadin kan yankunan mashigin teku na Bac Bo. A cikin sanarwar da aka bayar a karshen taron, an ce, ya kamata, kasar Sin da kungiyar ASEAN su hada kansu a fannin aikin masana'antu da cinikayya da zuba jari don gaggauta raya yankuna da ke zagayen mashigin teku na Bac Bo.

Malam Van Der Linden, mataimakin shugaban bankin raya Asiya ya bayyana a kan wannan cewa, "ana sa ran alheri ga hadin kan tattalin arziki a mashigin teku na Bac Bo. Yanzu, mun riga mun zuba jari wajen shimfida babbar hanyar mota a jihar Guangxi ta kasar Sin wadda ke hada kasashen Sin da Vietnam. Hanyar nan tana da matukar muhimmanci ga jihar nan, kuma ga hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Vietnam. Sabo da haka bankin raya Asiya yana matukar son, ya ci gaba da zuba jari wajen gudanar da shirin gina hanyoyi da tashoshin jiragen ruwa, don gaggauta raya yankin mashigin teku na Bac Bo."

Babbar hanyar mota da Malam Linden ya ambata wata babbar hanyar mota ce da ta tashi daga birnin Nanning, fadar gwamnatin jihar Guangxi, ta tsaya a wani wuri mai suna "Youyiguan" da ke kan bakin iyaka tsakanin kasashen Sin da Vietnam. Bayan da aka kaddamar da wannan babbar hanyar mota, an samar da dama ga kara bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN. Malam Chen Wu, mataimakin shugaban jihar Guangxi ta kasar Sin ya ce,

"bisa shirinmu, za a shimfida babbar hanyar jirgin kasa da ta mota wadanda za su tashi daga birnin Nanning na jihar Guangxi ta kasar Sin, su biyo ta birnin Hanoi na kasar Vietnam, da birnin Vientiane na kasar Laos, da birnin Bangkok na kasar Thailand, da birnin Kuala Lumpur na kasar Malasiya, har ta zo kasar Singapore. Idan an gina irin wannan babbar hanyar jirgin kasa da ta mota, to, za a sami babban taimako daga wajensu don bunkasa tattalin arziki a wurare da ke bakin hanyar da raya kasashe da ke zagayen hanyar."

Ban da hanyar jirgin kasa da ta mota, kuma ana aikin wurjanjan wajen gina tashoshin jiragen ruwa a birane da ke zagayen mashigin teku na Bac Bo. Malam Cao Yushu, wani jami'in majalisar gudanarwa ta kasar Sin yana ganin cewa, inganta hadin kan tattalin arziki a yankin mashigin teku na Bac Bo, yana da matukar muhimmanci ga raya wurare da ke yammacin kasar Sin. Ya ce, "wani dalilin da ya sa wurare na yammacin kasar Sin sun yi baya-baya wajen bunkasa tattalin arziki idan an kwatanta su da sauran wurare na kasar Sin, shi ne domin mashigin teku na Bac Bo mashigin teku ne daya kurum a wadannan wurare na kasar. Jihar Guangxi tana yankin mashigin teku na Bac Bo, kuma tana daya daga cikin jihohi da ake kokarin raya su a yammacin kasar Sin. Sabo da haka bunkasa tattalin arziki a wurare da ke zagayen mashigin teku na Bac Bo yana da matukar muhimmanci ga raya wauraren da ke yammacin kasar Sin. " (Halilu)