Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-06 18:22:38    
Maido da shawarwari a tsakanin manyan shugabanni na kasashen Sin da Japan zai bude kofar samar da damar kyautata huldar da ke tsakanin bangarorin biyu

cri
Bisa gayyatar da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi masa ne, sabon firayim ministan kasar Japan Shinzo Abe zai kai ziyarar aiki a kasar Sin daga ran 8 zuwa ran 9 ga wannan wata. Lokacin da kwararren kasar Sin kan batun da ke kasancewa tsakanin kasar Sin da kasar Japan Mr Yuan Zongze ya karbi ziyarar musamman da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya yi masa, ya bayyana cewa, ziyarar da zai yi don bude kofar samar da damar kyautata huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, manyan shugabannin kasashen biyu za su tabbatar da makomar raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, ziyarar ita ma za ta ba da taimako ga kara daga niyyar jama'a ta sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Japan.

Dalilin da ya sa huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan ta shiga halin kaka-ni-ka-yi shi ne saboda tsohon firayim ministan kasar Japan Junichiro Koizumi ya kai ziyarar nuna ban girma a haikalin Yasukuni kiri da muzu.

A shekaru 30 na karnin da ya shige, kasar Japan ta kai wa kasar Sin hari, bisa sakamakon nan ne sojoji da jama'ar farar hula na kasar Sin da yawansu ya kai miliyan 35 ko fiye sun mutu , yawan darajar dukiyoyin kasar Sin ya yi hasara da yawansu ya kudin Amurka dalla biliyan 600. Amma, bayan shekarar 2001 da tsohon firayim ministan kasar Japan Junichiro Koizumi ya hau kujerar mulki, sai ya kai ziyarar nuna girmamawa ga 'yan furusunonin na yakin duniya na biyu da ke da laifi bisa matsayin A a haikalin yasukuni har sau 6 a jere.

Aikin da Junichiro Koizumi ya yi ya jawo suka sosai daga wajen kasashen Asiya da yawa, ciki har da kasar Sin da kasar Korea ta Kudu, wannan ya karya inda bai kamata a kai ba wajen lahanta huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, saboda haka yawan tsawon rashin ganawar da ke tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu wato Sin da Japan ya kai shekaru 5 da rabi ko fiye.

Ba sau daya ba ba sau biyu ba shugabannin kasar Sin sun bayyana cewa, in shugabannin kasar Japan suka yi alkawari a bayyane na dakatar da ziyarar nuna girmamawa a haikalin Yasukuni, sai bangaren kasar Sin yana son yin tattaunawa da ganawa a tsakaninsa da su. A lokacin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci taron shugabanni na 6 na kasashen Asiya da Turai da aka shirya ba da dadewa ba, ya bayyana cewa, da ya ke shugabannin gwamnatin kasar Japan ba su kula da sukar da jama'ar kasar Sin da jama'ar kasashen Asiya suke yi, sau da yawa ne suka kai ziyarar nuna girmamawa a haikalin yasukuni, saboda haka wannan ya bata ransu sosai da sosai, kuma ya kafa katangar siyasa ga raya huldar da ke tskanin kasar Sin da kasar Japan.

Bangaren kasar Sin yana ta sanya kokarin kyautata huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, a sa'I daya kuma a kwanakin da ba su cika goma ba da sabon firayim ministan kasar Japan Shinzo Abe ya hau kujerar mulki, sai ya yi shelar kai ziyara a kasar Sin.

Game da ziyarar nan, kwararren kasar Sin kan batun da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasar Japan kuma mataimakin shugaban hukumar yin nazari kan batutuwan kasa da kasa na kasar Sin Mr Yuan zongze ya bayyana cewa, yanzu, babbar matsalar da ke kasancewa kuma kamata ya yi a daidai ta ita ce, wane irin manufar da za a bi don raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan lami lafiya tare da yin hadin guiwar sada zumunta? Babban abu shi ne ya kamata a tsai da babbar ka'idar raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu a nan gaba da kuma kago wani halin da ake ciki na kara inganta huldar hadin guiwa tare da samun sakamako.

A lokacin da Abe ya shiga ayyukan yin takarar zaman firayim ministan kasar Japan, ya taba bayyana cewa, yana son yin kokarin raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, kuma ya amince da hakikanan abubuwan da kasar Japan ta yi na kai wa kasashen Asiya da yawa hari ,, bayan da ya hau kujerar mulki, sai ya amince da sakamakon hukuncin da kotun soja na Gabas ta tsakiya ta kasashen duniya ta yanke wa kasar Japan, bai kamata ba kasar Japan ta yi shakkar sakamakon nan.

Amma abin da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne, Mr Abe bai bayyana ra'ayinsa sosai a kan batun kai ziyarar nuna girmamawa da firayim ministan kasar Japan ya yi a haikalin Yasukuni ba, Mr Yuan ya bayyana cewa, wannan ya bayyana cewa, b a a tabbatar da cewa, Mr Abe ba zai kai ziyarar nuna girmamawa a haikalin Yasukuni ba. (Halima)