Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-05 17:08:13    
Bayyanin kan Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 na Lardin Liaoning

cri

A farkon 'karni na 21 , kasar Sin ta kafa cikakken tsarin tattalin arziki na kasuwancin gurguzu . Kuma ta fara shiga muhimmin lokaci don tabbatar da tsarin musamman na 3 . A cikin wannan lokaci . Lardin Liaoning ya kyautata fasalin tattalin arzikinsa . Kuma ta kara saurin bunkasa tattalin arziki da ci gaban zaman al'umma . Gwamnatin Lardin Liaoning ta tsara kuma tana aiwatar da Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 kan tattalin arziki da zaman al'umma na Lardin Liaoning . Wannan shirin yana da babbar ma'anar tarihi .

Lardin Liaoning yana daya daga cikin larduna 3 dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin 4 dake karkashin gwamnatin kasar Sin .

Lardin Liaoning yana da wadatattun albarkatu . Fadin gonakai ya kai muraba'in kadada dubu 1480 , wato ya kai kashi 4.7 cikin 100 na duk fadin kasar Sin . A Lardin Liaoning za a iya bunkasa masana'antun man fetur da masana'antun kera magunguna .

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , Saboda tattalin arzikin kasar Sin ta sami yalwatuwa da saurin gaske kuma cikin dogon lokaci , shi ya sa a cikin 'yan shekarun da suka wuce , a nan kasar Sin an bullo da halin karancin wutar lantarki wanda ba a taba ganinsa ba a tarihi . A yanayin zafi na wannan shekara , galibin wuraren kasar Sin suna fuskantar halin karancin wutar lantarki . Saboda haka Wurare daban daban na Kasar Sin za su dauki matakai masu yawa don sassauta matsalar karancin wutar lantarki , kuma a kan tushen tabbatar da yawan wutar lantarkin da ke samar ga zaman yau da kullum na jama'a , za a biya bukatun sassa daban daban na zaman al'umma a wajen yin amfani da wutar lantarki .

A watanni 3 na farko na wannan shekara , yawan tashoshin ba da wutar lantarki na larduna wadanda suka dauki matakan kayyade yawan amfanin wutar lantarki ya kai 26 . Lardin Liaoning yana daya dake cikinsu . Daga karshen watan Yuni , wurare Masu yawa na kasar Sin sun bullo da yanayi mai zafi sosai, har ya yi sanadiyyar 'karuwar amfani da wutar lantarki . Alal misali a Lardin Liaoning , yawan wutar lantarkin da aka yi amfani a wajen bude iyakwandishin ya kai kimanin kashi 40 cikin 100 na jimlar wutar lantarkin , saboda haka an kara sabanin samar da wutar lantarki . Kamfanin ba da lantarki na kasar Sin ya kimanta cewa , a yanayin zafi na wannan shekara a duk kasar za a yi karancin lantarki na kilowatt miliyan 25. Don sassauta halin karancin wutar lantarki da tabbatar da aikin samar da wutar lantarki , wurare daban daban na kasar Sin sun dauki matakai masu yawa . Lardin Liaoning yana daya daga cikinsu.

Li Zhiguo , kakakin watsa labaru na Kamfanin ba da wutar lantarki na Lardin Liaoning ya bayyana cewa , tun daga watan Satumba na shekarar bara , kamfaninsa ya fara aikin share fagen samar da wutar lantarki a wannan shekara .

Mr. Li ya ce , mun tattara kudin Sin Yuan fiye da biliyan 2 don kyautata manyan ayyukan ba da wutar lantarki , kuma a kafin ran 30 ga watan Yuli na wannan shekara mun gama ayyukan . A

yanayin zafi, wadannan ayyukan sun ba da taimako kwarai da gaske .

Ban da Lardin Lioaning , hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin da sauran wurare su ma sun yi aikin share fage sosai don magance lokacin yin amfani da wutar lantarki mai yawa a yanayin zafi . A watanni 6 na farko na wannan shekara , Kamfanin ba da lantarki na kasar Sin ta gina manyan hanyoyin ba da wutar lantarki na kilomita fiye da dubu 5 . Ta haka an kara karfin samar da wutar lantarki .

A wajen samar da wutar lantarki , wurare daban daban na kasar Sin suna bin wata manufar cewa , da farko dai za a samar da wutar lantarki ga zaman yau da kullum na jama'a .

Song Jin , mataimakin babban manajan Kamfanin ba da wutar lantarki na Lardin Liaoning ya bayyana cewa , don kasa kayyade amfanin wutar lantarki da tabbatar da aikin samar da wutar lantarki ga farar hula , a wannan shekara mun yi aikin musamman don kula da bukatar jama'a . Mun tsara wani shirin wanda ya jibinci masana'antu fiye da dubu 30 .

Abin da kuka saurara dazu nan shi ne labarin kasa kan Lardin Liaoning . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan makamashin Lardin . Kwanan baya gwamnatin Liaoning ta kira taron aiki kan yadda za a yi tsimin makamashi . Li Keqiang , sakataren Kwamitin jam'iyyar Liaoning da Zhang Wenyue , shugaban Lardin Liaoning sun yi jawabi daya bayan daya kan aikin tsimin makamashi . Mr. Zhang ya jaddada cewa , za mu yi kokari don mai da lardin Liaoning da ya zama lardi mai tsimin makamashi kuma yana kasancewa da muhalli mai kyau da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci .

Zhang Wenyue , Shugaban Lardin Liaoning da WangHongliang , mataimakin shugaban Lardin su kuma sun yi jawabi , inda suka bayyana cewa , A ran 2 ga watan Satumba a nan birnin Shengyang , An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar Lardin Liaoning . Taron ya zartas da Shirye-shiryen raya tattalin arzikin birnin da zaman al'umman Liaoning a shekaru 5 masu zuwa da rahoton aikin gwamnati .

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin Lardin Lioaning na shekara-shekara zai kai kashi 9 cikin 100 . Kuma an tabbatar da manufar rage yawan makamashin da za a yi amfani da rage yawan gurbatattun abubuwan da za a fitar da su . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kafa sababbin kauyyuka da hanzarta gyare-gyaren tattalin arziki da ciyar da Bunkasuwar birane da gundumomi cikin daidaici , za su zama tsarin musamman da manyan ayyukan Lardin Liaoning.

Muna muku marahabin domin sauraren shirinmu na Me Ka sani game da kasar Sin .

Mr. Zhang , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta lardin Liaoning Ya yi nuni da cewa , a wajen kiyaye ikon musamman na lambobin kasuwanci da aka rajista , Lardin Liaoning tana mai da hankali sosai kan lambobin kasuwanci na kasar Sin da na kasashen waje .

Ya kuma bayyana cewa , a cikin shekaru 5 da suka shige , mun dauki aikin kiyaye shahararrun lambobin kasuwanci na kasashen waje kamar wani muhimmin aiki na Lardin Liaoning . Musamman ma daga shekarar 2004 zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara , Ofishin lambobin kasuwanci da Kwamitin duba lambobin na hukumar sun yi amincewa da shahararrun lambobin kasuwanci guda 30 na kasashen waje .

Kasar Sin tana daya ce daga cikin kasashe masu fama da lambobin jebu a duniya . Bayan da aka shiga sabon karni , kasar Sin ta dauki matakan magance laifufkan kera lambobin jebu .

A gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 15 ga wata a nan birnin Beijing , Li Dong, shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta Lardin Liaoning ya ce , kasar Sin ta yi na'am da wadannan shahararrun lambobin kasuwanci kuma tana kiyaye ikon mallakar ilminsu , ta sami yabo sosai daga masana'antu masu yawa musamman ma wasu manyan kamfanonin ketare kuma sun karfafa amincewar aikin kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasar Sin . Saboda haka , kasar Sin ta jawo hankulan kasashe masu yawa su zo nan kasar Sin don rajista lambobinsu . Mu ma haka , Lardin Liaoning zai aiwatar da manufar gwamnatin kasar Sin , kuma za mu mai da hankali sosai kan kananan fannoni.(Ado)