Tambayar da za mu amsa a yau ta fito ne daga hannun malama Amina Abubakar, mazauniyar birnin Abuja na kasar Nijeriya. A cikin wasikar da ta aiko mana, ta ce, shin Sinawa suna da wasu bukukuwa na gargajiya? Masu sauraro, kasar Sin kasa ce da ke da dadadden tarihi. A cikin shekaru dubu dubai da suka wuce, jama'ar da ke zaune a nan kasar, sun fitar da bukukuwan gargajiya da yawa wadanda suka bayyana halayen musamman na al'adun kasar Sin. Ranar 6 ga watan nan da muke ciki kuma, wato ran 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, rana ce ta yin bikin gargajiya na murnar tsakiyar yanayin kaka a nan kasar Sin, to, a cikin shirinmu na yau kuma, bari mu bayyana muku bikin nan na gargajiyar kasar Sin, wato bikin tsakiyar yanayin kaka.
Bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ranar 15 ga wata na takwas na ko wace shekara, rana ce ta yin bikin tsakiyar yanayin kaka, wanda ya kasance na biyu daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na kasar Sin, wato bayan bikin yanayin bazara. Sabo da ana yin bikin ne a daidai lokacin tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ana kiransa bikin tsakiyar yanayin kaka. Bayan haka, a ran nan da dare, wata ya fi kewayayye da kuma haske, ga shi kuma mutanen zamanin da sun dauki kewayayyen wata a matsayin alamar sake haduwar iyali, shi ya sa ana kuma kiran bikin 'bikin haduwar iyali'. Bikin tsakiyar yanayin kaka yana da dogon tarihi a nan kasar Sin, tun tuni a farkon zamanin daular Tang, ya riga ya zama wani zaunannen bikin da aka yi, daga baya a lokacin daular Song kuma, ya fara samun karbuwa sosai.
Game da asalin bikin nan na tsakiyar yanayin kaka, ana tattare da ra'ayoyi biyu. Wato da farko, ana ganin cewa, bikin yana da nasaba da girbin amfanin gona da ake yi a lokacin kaka. Sabo da kasar Sin kasa ce ta aikin noma, shi ya sa a yayin da mutanen zamanin da suke shuke-shuke, su kan yi ibada ga gumakan filayen kasa, don roko a ba su girbi mai kyau. Da lokacin girbi ya yi kuma, su ma su kan yi biki, don nuna godiya ga gumaka. Ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, lokaci ne da shimkafa ta nuna, shi ya sa iyalai daban daban su kan yi ibada ga gumakan filayen kasa, shi ya sa ana ganin cewa, watakila bikin tsakiyar yanayin kaka al'ada ce ta gargajiya ta nuna godiya ga gumakan filayen kasa don girbi mai kyau da suka kawo, kuma daga baya ya yi ta bunkasa. Amma akwai wani ra'ayi daban da ke nuni da cewa, bikin yana da nasaba da al'adar bauta wa wata da mutanen zamanin da suka yi, kuma yana da nasaba da tsohon imanin da mutane ke da shi ga wata.
To, amma me Sinawa suke yi a bikin nan na tsakiyar yanayin kaka? A cikin shekaru aru aru da suka wuce, jama'ar kasar Sin sun sami al'adu iri iri dangane da bikin. Idan mu tabo magana a kan al'adun bikin tsakiyar yanayin kaka, to, abin da bai kamata mu rasa ba shi ne wainar wata. Cin wainar wata a gun bikin tsakiyar yanayin kaka al'ada ce ta gargajiya ta Sinawa. Ga shi wainar kewayayya ce, wanda ke alamanta haduwar iyali, ya bayyana buri mai kyau na jama'a dangane da samun sake haduwar iyali. A lokacin bikin, iyalai su kan hadu, suna cin wainar wata, kuma suna zuba ido ga wata, suna hira suna jin dadi.
An ce, da ma wainar wata abin ne da aka bauta wa gunkin wata, amma daga bisani, jama'a sun mayar da zuba ido ga wata a bikin tsakiyar yanayin kaka da cin wainar wata a matsayin alamar haduwar iyali, shi ya sa sannu a hankali wainar wata ita ma ta zama abin kyauta da ake bayar wa a bikin. A cikin dogon lokaci kuma, wainar ta yi ta bunkasa, har ma ta sami ire-ire masu yawa. Bambancin wurare daban daban shi ya sa wainar ke da siffofi da dandano iri iri. Ban da wannan, 'ya'yan itatuwa iri iri su ma abinci ne da ba a iya rasa su ba a gun bikin.
A lokacin bikin tsakiyar yanayin kaka, wata ya kan fi girma da kewayayye da kuma haske, sabo da haka, ban da cin wainar wata, zuba ido ga wata da ba da ibada ga wata su ma muhimman al'adu ne na Sinawa. (Lubabatu)
|