A ran 3 ga wata, a hukunce ne, an kaddamar da tashar internet ta gwamnati ta taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da kuma taron ministocinsu a karo na 3.
Sunan wannan tashar internet shi ne www.focacsummit.org, ana iya karanta shafinsa cikin Sinnanci da Turanci da kuma Faransanci. Wannan tashar internet ta yi shirye shirye fiye da goma kamar labaran dumi dumi da sharhi na bangarori daban daban da yin mu'amalar aminci da dai sauransu. Wannan tashar internet za ta watsa labarai a kan manyan ayyukan da ake yi a gun taron da manyan jawabai da shugabanni suke yi da manyan takardu da ake zartas a gun taron da dai sauransu. Ban da wannan kuma, wannan tashar internet za ta yi bayyanai a kan dandalin tattaunawar da tarihinsa da mambobinsa da tarurrukan da ya yi a da da kuma wasu manyan ajiyayyun bayanoni.
Domin kara zurfafa aminci na gargajiya da kara hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, bangarorin biyu sun yi shawarwari kuma sun yanke shawarar shirya taron koli a Beijing na dandalin tattaunawa a tsakanin Sin da Afirka da kuma taron ministocinsu a karo na 3 daga ranar 3 zuwa ranar 5 ga watan gobe. Babban taken wannan taro shi ne 'aminci da zaman lafiya da hadin kai da kuma samun bunkasuwa'.(Danladi)
|