Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-04 16:51:17    
Bikin tsakiyar kaka na kasar Sin

cri

Ranar 6 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki ranar 15 ga watan Augusta ce ta kalandar noma ta kasar Sin, kuma biki ne mafi muhimmanci na gargajiyar kasar Sin wato bikin tsakiyar kaka. A wannan rana, bisa al'adar mutanen kasar Sin, duk yawan mutanen iyalai suna taruwa gu daya, suna jin dadin kallon wata mai cika kuma mai haske sosai, suna yi wa juna gaisuwar ganawa da juna da fatan alheri.

Bikin tsakiyar kaka na kasar Sin yana da nasaba da kalandar noma sosai da sosai. Bisa kalandar noma ta kasar Sin, watan Augusta yana tsakiyar yanayin kaka, amma ranar 15 tana tsakiyar watan Augusta, saboda haka ana kiran ranar 15 ga watan Augusta da cewar wai tsakiyar kaka ce. Ana ganin cewa, a wannan rana, in mutane suna kallon wata daga duniya, sai watan da suka tsinkaya ya cika sosai kuma mafi girma ne tare da haske sosai . A kasar Sin, mutane sun yi shagulgula da yawa don murnar bikin duk bisa abubuwa dangane da wata , wasu suna yin bikin girmama wata, wasu suna yin addu'a domin wata, wasu kuma suna jin dadin kallon wata da dai sauransu.

Masomin bikin tsakiyar kaka shi ne daga bikin girmama wata da aka yi a zamanin aru aru na kasar Sin. Tsofaffin littattafai na zamanin aru aru sun tanadi cewa, an soma maganar "tsakiyar kaka" kafin shekaru dubu 2 da suka wuce, a wancan zamani, an riga an tsai da tsari cewa, sarakuna sun shirya bikin girmama rana a yanayin bazara, kuma sun shirya bikin girmama wata a yanayin kaka don yin addu'a da fatan samun girbi mai armashi. Mutanen zamanin aru aru sun bayyana cewa, idan babu raban da wata ya samar mana ba da kuma babu watan da ya yi mana lissafin sa'o'in aikin noma, to ba za mu iya samun girbi mai armashi ba. Wani mashahurin dakali mai suna Yuetang dake birnin Beijing shi ne wurin da sarakunan zamanin aru aru suke yi bikin girmama wata. A wajen mutanen kasar Sin, an kafa dakali da rumfuna da gidaje masu benaye na nuna girmamawa ga wata da sauran gine-ginen tarihi da yawa, kuma an yada tatsuniyoyi da almarori da yawa dangane da wata.

Bikin tsakiyar kaka ya zama bikin jama'ar farar hula tun daga karni na 7 da kafa daular Tang ta kasar Sin, an bayyana cewa, wannan na da nasaba da wani mashahurin sarkin daular Tang na kasar Sin mai suna Tang Xuanzong.

An yada cewa, sarkin Tang Xuanzong ya kware sosai wajen fasahohi, yana da sha'awar jin dadin kallon wata sosai. A ranar 15 ga watan Augusta na wata shekara, ba zato ba tsammani sarki Tang Xuanzong ya yi tsammanin zuwan wata don yawon shakatawa. Saboda haka ya yi mafarkin zuwan wata bisa taimakon fasahar aljanna da aka yi masa, ya sauka a gaban wata fadar da aka kafa mata allo tare da kalmomin da ke cewa, "Guanghangong", wato ma'anarta ita ce fadan da ke da sanyi sosai. Wasu angel suna rawa tare da kade-kade masu dadin ji sosai , Tang Xuanzong yana kallo yana manta da kome da kome. Bayan da ya farka daga mafarkinsa, sai ya wallafa wata kida mai dadin ji sosai ta hanyar yin amfani da kade-kaden da ya ji a cikin mafarkinsa, kidan nan na da lakabi haka, kidan tufaffi masu kyaun gani sosai da aka yi da gasu, kidan nan ya zama kida ne da aka yada shi daga zuri'a zuwa zuri'a .sa'anan kuma jama'ar farar hula suna kwaikwayon abin da sarkin ya yi, in wata ya cika a ranar 15 ga watan Augusta bisa kalandar noma, sai duk mutanen iyali suka taru gu daya don jin dadin kallon wata mai haske sosai da yin sauran shagulgula.

Wata irin waina da mutanen kasar Sin suka ci a bikin tsakiyar kaka ita ce Yuebing, an dafa Yuebing ta hanyar yin amfani da sukari da ridi da gyada da garin wake da dai sauransu, a fuskarta, an manna mata da zane tamkar yadda sifar wata , sa'anan kuma an yanke ta kashi kashi, an rarraba su ga mutanen iyalin, kowa zai sami kashi daya, in wani ba ya gida , a kan ajiye wani kashin waina gare shi don bayyana cewa, duk mutanen iyalin suna taru gu daya, a ranar bikin tsakiyar kaka, in wata ya fito, to ana shimfida abinci da 'ya'yan itatuwa da sauransu a kan teburori domin wata, duk domin nuna fatan alheri da neman zaman jin dadi. A farkon shekarar da muke ciki, an riga an maido da bikin tsakiyar kaka don ya zama bikin da ke wakiltar abubuwan al'adun tarihi ba na kayyayaki ba na kasar Sin.(Halima)