Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-04 16:49:27    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(28/09-04/10)

cri

An rufe babban taron kafofin yada labaru na duniya a karo na farko domin taron wasannin Olympic na Beijing a ran 28 ga watan Satumba. A gun taron da aka yi kwanaki 2 ana yinsa, wakilai fiye da 300 na kamfanonin dillancin labaru da jaridu da mujalloli na kasashen duniya da kuma 'yan kwamitin yada labaru na kwamitin wasannin Olympic na duniya da hukumomin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da abin ya shafa sun yi mu'amala da tattaunawa kan watsa labaru kan taron wasannin Olympic na shekarar 2008 da kuma ba da hidimomi ga kafofin yada labaru. A gun taron da aka yi, jami'an hukumomin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun yi karin haske kan ci gaban ayyukan shirya taron wasannin Olympic na Beijing da kuma hidimomin da za a ba kafofin yada labaru, sa'an nan kuma sun yi cudanya da wakilai masu halartar taron kan gine-gine da hidimomin da kafofin yada labaru za su bukata wajen watsa labaru kan taron wasannin Olympic na shekarar 2008.

A cikin karon karshe na gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 ta maza ta gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da aka yi a birnin Daegu na kasar Korea ta Kudu a ran 28 ga watan Satumba, dan wasa mai suna Liu Xiang daga kasar Sin ya lashe dan wasa mai suna Allan Johnson daga kasar Amurka da dakikoki 13 da motsi, ta haka ya zama zakara, Allan Johnson kuwa ya zama na biyu.

Wannan karo ne na hudu da Liu Xiang ya kara da Allan Johnson a cikin kwanaki 18 da suka wuce. A cikin dukan karon karshe na gasanni 4 da suka yi, Liu Xiang ya lashe Allan Johnson sau 3.

Ran 28 ga watan Satumba, a gun dandalin tattaunawa kan iyalan masu nakasa a kwakwalwarsu da birnin Shanghai ya shirya a shekarar 2006, mataimakin kwamitin wasannin Olympic na musamman na duniya wato kwamitin SOI ya bayyana cewa, raya wasannin Olympic na musamman yana matukar bukatar goyon baya daga mambobin iyalan masu nakasa a kwakwalwarsu, sa'an nan kuma, yin cudanya a tsakanin iyalan masu nakasa a kwakwalwarsu ya iya ingiza bunkasuwar wasannin Olympic na musamman sosai.(Tasallah)