Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-04 16:47:49    
Kasar Sin ta kyautata halayyar wayewar kai na masu yawon shakatawa nata domin taron wasannin Olympic mai zuwa

cri

Kowa ya sani, za a yi taron wasannin Olympic a nan Beijing a shekarar 2008, don nuna ladabin kasar Sin, ana gudanar da aikin kyautata halayyar wayewar kan masu yawon shakatawa na kasar Sin a duk kasar.

Birnin Beijing da kasar Sin tana jawo masu yawon shakatawa na kasashen waje saboda wuraren shakatawa masu yawa. Ko shakka babu Beijing za ta kara jawon hankulan mutane domin yin taron wasannnin Olympic a nan. Amma harkokin rashin da'a da wasu masu yawon shakatawa na gida suke yi sun kawo illa ga kyakkyawar siffar kasar Sin a gaban mutanen kasashen waje, sun kuma jawo hankulan akasarin ra'ayin jama'a na gida da na waje da kuma sukansu.

Don canja irin wannan halin da ake ciki yadda ta kamata, hukumomin kasar Sin da abin ya shafa sun yi shekaru 3 suna kyautata halayyar wayewar kan mutanen kasar Sin a fannin yawon shakatawa a duk kasar tun daga kwanaki 10 na tsakiya na watan Agusta na wannan shekara, tabbas ne za a sami sakamako kafin taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Za a dora muhimmanci kan gyara rashin da'a da mutanen kasar Sin za su yi a lokacin yawon shakatawa, ta yadda za a kyautata halayyar wayewar kan mutanen Sin wajen yawon shakatawa a bayyane.

Jama'ar kasar Sin masu yawa suna ganin cewa, kyautata halayyar wayewar kan mutanen Sin wajen yawon shakatawa ya zama abin da ya zama wajabi ne sosai. Madam Song Li, wadda ke aiki a cikin wani kamfani mai jarin kasashen waje, ta bayyana cewa,

'Na kan yi yawon shakatawa tare da mutanen kasashen waje. Amma a wurare da yawa, wasu mutanen Sin ba su mai da hankulansu kan halayyar wayewar kansu ba. Na ji kunya sosai, musamman ma a lokacin da nake yin rakiyar mutanen kasashen waje, wannan ya kawo illa ga siffofin Sinawa. Taron wasannin Olympic na shekarar 2008 yana zuwa, wajibi ne mu nuna kyakkyawar halayya. Ina tsammani cewa, dole ne dukanmu mu fito da al'ada mai nagarta, ta haka za mu nuna sabuwar siffar Beijing ga kasashen waje. '

A kwanan baya hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ta tattara misalan tabi'u na rashin da'a da shawarce-shawarce kan kyautata halayyar wayewar kan mutanen Sin wajen yawon shakatawa, za ta kuma wallafa littattafai kan yawon shakatawa a gida da waje bisa shawarce-shawarce da misalan da ta tattara. Kafin ran 1 ga watan Oktoba na wannan shekara, za ta ba su ga masu yawon shakatawa da za su yi yawon shakatawa cikin kungiyoyi

Ban da wannan kuma, a kwanan nan hukumar yawon shakatawa ta birnin Beijing ta gabatar da sabuwar ka'idar cewa, kafin zuwa yawon shakatawa, ban da wasu bayanan yau da kullum kuma, za a horar da masu yawon shakatawa a fannin ladabi na yawon shakatawa. Madam Liu Yunhui, wadda ke aiki cikin ofishin harkar yawon shakatawa na Kang Hui na Beijing, ta yi bayani kan ra'ayinta kan wannan sabuwar ka'ida, ta ce,

'A ganin ofishinmu, wannan sabuwar ka'ida tana da kyau kwarai. Dalilin da ya sa wani mutum ba shi da da'a shi ne domin ba shi da halayyar wayewar kai. Wannan za a kawo illa ga siffar kasarmu. Za a yi taron wasannin Olympic a nan Beijing a shekarar 2008, wannan dama ce da ba a taba samunta a cikin shekaru 1000 ba, haka kuma wata dama ce da mutanenmu za mu yi amfani da ita wajen nuna halayyarmu a gaban kasashen waje. Shi ya sa horar da mutane wajen ladabi na yawon shakatawa yana da muhimmanci sosai.'

Yanzu masu yawon shakatawa da suka yi yawon shakatawa a kasashen waje sun nuna siffar kasar Sin a gaban kasashen waje Mr. Chen Chong, wani dan yawon shakatawa, ya gaya wa manema labaru cewa,

'A zahiri kuma mutane sun nuna siffar kasarsu a lokacin da suke kasashen waje. A duk lokacin da nake yawon shakatwa a waje, masu ja gorar yawon shakatawa su kan tuna mana da abubuwan da ya kamata mu mai da hankali a kai. A ganina, horar da masu yawon shakatawa a fannin ladabi kafin su tashi yana da kyau, ta haka za a sanya masu yawon shakatawa su kara mai da hankulansu kan wannan fanni, haka kuma za su kyautata halayyarsu. Wannan yana da matukar muhimmanci a fannonin maraba da taron wasannin Olympic na shekarar 2008 da kuma nuna siffofin Sinawa.'

Halayyar wayewar kan masu yawon shakatawa ya ba da tasiri kan siffar wata kasa a gaban kasashen duniya, shi ya sa ko wane Basinne ya mai da hankali a kan ladabi, ta yadda zai ba da gudummuwa wajen ci nasarar yin taron wasannin Olympic na Beijing.(Tasallah)