Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-03 20:39:34    
Afirka tana cin gajiyar taro wajen raya tattalin arziki

cri
Kwanan baya, mutane suna rububin zuwa birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya domin halartar taron koli na duniya kan samun aikin yi da aka shirya domin matasa da kuma taron koli na harkokin birane na Afirka. Yawan mutanen kasashen waje da suka halarci wadannan taruruka 2 ya wuce 10,000. Bayan tarurukan 2, masu halartar taron su kan yi yawon shakatawa a wuraren shakatawa na kasar Kenya, kamar shehakarren gidan dabbobin daji na Masai Mara, saboda haka su kan kawo wa kasar Kenya kudade masu yawa ta hanyar yawon shakatawa.

A lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin kan wannan fanni a kwanan baya, darektan sashen harkokin kasuwanci na hukumar harkokin yawon shakatawa ta kasar Kenya ya bayyana cewa, kasar Kenya ta sami riba ne daga wajen tattalin arziki da kasashen Afirka suke raya ta hanyar yin taruruka, sa'an nan kuma, kasashen Afirka suna da babban karfin da ba su taba yin amfani da shi ba wajen raya tattalin arzikinsu ta hanyar shirya taruruka, ana sa ran alheri kan makomarsu.

Bisa labarun da kafofin yada labaru na kasar Kenya suka bayar, an ce, an yi manyan tarurukan duniya guda 132 a kasashen Afirka a shekarar bara, kasashen Afirka ta Kudu da Masar da Morocco da Kenya kasashen Afirka ne da aka fi shirya tarurukan duniya a wajensu. An nuna cewa, a cikin shekaru masu zuwa, matsakaicin yawan saurin karuwar tattalin arzikin duniya da za a raya ta hanyar shirya taruruka zai kai kashi 4 cikin dari a ko wace shekara, ana kuma sa ran cewa, kasashen Afirka za su ci riba mafi yawa daga wajen saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya da aka raya ta hanyar yin taruruka.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu an yi manyan tarurukan duniya da yawansu ya kai kashi 2 cikin dari a kasashen Afirka kawai, an yi irin wadannan taruruka da yawansu ya kai kashi 58 cikin dari a kasashen Turai, ko ta yaya ba za a iya kwatanta su tare ba. Amma wannan ya nuna cewa, kasashen Afirka suna da babban karfin da ba su taba yin amfani da shi ba wajen raya tattalin arzikinsu ta hanyar shirya taruruka. Yanzu kasashen Afirka suna kara tabbatar da kwanciyar hankali a fuskar siyasa, suna kuma kara bunkasa tattalin arzikinsu yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, saboda sun rika kyautata manyan ayyuka da kuma hidimomin da za su samar domin taruruka, mutane suna kara fahimtar kasashen Afirka, shi ya sa za a kara yin manyan tarurukan duniya a kasashen Afirka.

Kasar Kenya ta gwada misali mai kyau. An shirya wasu muhimman tarurukan duniya a kasar a shekarar bana. Saboda yanayi na da kyau a nan, kasar Kenya tana da albarkatun dabbobin daji, ta kuma bunkasa harkokin yawon shakatawa da hotel lami lafiya, dukansu sun samar da sharadi mai kyau gare ta wajen raya tattalin arziki ta hanyar shirya taruruka.

Amma wannan darekta ya bayyana cewa, da kyar mutane su canja ra'ayoyinsu kan kasashen Afirka cikin gajeren lokaci ba, a ganinsu, kasashen Afirka a baya ne suke, suna fama da talauci, wannan babban cikas ne ga kasashen Afika a fannin raya tattalin arzikinsu ta hanyar yin taruruka. An yi taron kara wa juna sani kan yadda za a ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Afirka ta hanyar yin taruruka a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a watan Agusta na wannan shekara, inda masu halartar taron suke ganin cewa, ya kamata a tanadi canja siffar Afirka cikin ajandar ayyuka. Ban da wannan kuma, sun yi babban taro kan harkokin yawon shakatawa na Afirka a karo na 1 a birnin Geneva na kasar Switzerland tun daga ran 10 zuwa ran 15 ga watan Satumba, inda masu halartar taron suke fatan za a yi kokari wajen nuna wa kasashen duniya kyakkyawar siffar Afirka.

Wannan darekta ya nuna cewa, shirya manyan taruruka zai iya sa kami kan bunkasuwar harkokin kasuwanci da na yawon shakatawa da sufuri da dakunan cin abinci da kuma hotel da sauran sana'o'in da abin ya shafa na wuraren, inda aka yi taruruka, kwararrun da abin ya shafa suna kira da a tanadi raya tattalin arziki ta hanyar yin taruruka a cikin shirin raya tattalin arziki da Kungiyar Tarayyar Afirka ta tsara. Ya kara da ewa, a lokacin kara yin furofaganda, tilas ne kasashen Afirka su gaggauta kyautata manyan ayyuka da kuma ya da da fasahar sadarwa, in ba haka ba, kasashen Afirka ba za su sami makoma mai kyau wajen raya tattalin arzikinsu ta hanyar shirya taruruka ba.(Tasallah)