Za mu gabatar muku da wani shahararren wurin shakatawa da ke arewa maso yammacin kasar Sin, sunansa kogunan dutse na Mo Gao. Kogunan dutse na Mo Gao tsohon wurin tarihi ne mai suna sosai a fannin addinin Buddha. An haka su a jikin tudun Mingsha da ke da nisan kilomita 25 a tsakaninsa da birnin Dunhuang na lardin Gansu a kudu maso gabas. An fara haka kogunan dutse tun daga shekarar 366. An ce, wata rana wani mabiyin addinin Buddha ya isa tudun Mingsha. Da ya ga haske na walkiya dubbai suna bullowa daga tudun Mingsha, yana tsammani cewa, wurin wuri ne mai tsarki, saboda haka ya haka kogo na farko a jikin tudun. Saboda an yi zamanin dauloli daban daban ana ta haka kogunan dutse, ya zuwa shekarar 1368, yawan kogunan dutse a nan ya kai misalin dubu, tun daga wannan shekara ne mutane ba su ci gaba da haka kogunan dutse ba.
Girman kogunan dutse na Mo Gao sun sha bambam, inda akwai mutum-mutumin Buddha manya da kanana a ciki. Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi kogunan dutse na Mo Gao a cikin takardar sunayen tsoffin wuraren tarihi na al'adu na duniya a shekarar 1987 da ta gabata.
Yanzu saboda kiyaye tsoffin wurare, an bude kogunan dutsen da yawansu bai kai 30 ba ga masu yawon shakatawa a nan, inda tilas ne masu yawon shakatawa su kai ziyara a karkashin jagorancin masu jagorar masu yawon shakatawa. Madam Liu Hongli, wadda ke jagorar masu yawon shakatawa, ta yi karin haske cewa, masu yawon shakatawa su kan kashe misalin sa'o'i 2 wajen ziyarar kogunan dutse fiye da 10, idan suna neman kai wa dukan kogunan dutsen da aka bude kofofinsu ga masu yawon shakatawa ziyara, to, za su bukatar kwana daya.
Madam Liu ya kara da cewa, da farko dai masu ja-gorar masu yawon shakatawa su kan ja gorar mutane zuwa ziyarar kogon dutse mai lamba 96. Dalilin da ya sa hakan shi ne domin an gina wata fada mai benaye 9 a wajen wannan kogon dutse. Wannan kogon dutse alama ce ta kogunan dutse na Mo Gao. Ta ce,
'Mutum-mutumin Buddha da aka saka a nan mutum-mutumin ne mafi girma a duk kogunan dutse na Mo Gao, lambarsa 96, ana kiransa 'babban mutum-mutumi da ke arewa'. An saka shi bisa siffar Buddha mai murmushi, wanda ke kula da makoma, tsayinsa ya kai mita 35.5, shi ne mutum-mutumin Buddha mafi girma a duk duniya, wanda aka ajiye shi a cikin daki.'
An haka kogon dutse mai lamba 96 a shekarar 695. Saboda an sha yin kwaskwarima kan mutum-mutumin Buddha da ke cikin wannan kogon dutse, shi ya sa wannan mutum-mutumin Buddha bai yi kamar yadda yake a lokacin da aka saka shi a farko ba, amma ya zuwa yanzu yana da kyaun gani sosai.
Ban da mutum-mutumin Buddha, zane-zanen jikin bango su ma muhimman kashi ne na fasahar kogunan dutse na Mo Gao. Ko da yake iska da rairayi sun yi shekara da shekaru suna kawo lahani gare su, amma wadannan zane-zanen jikin bango suna cikin hali mai kyau, har zuwa yanzu launinsu suna da kyaun gani. An yi yawancin zane-zane a jikin bango bisa labarun littattafan addinin Buddha. Siffofin da ke cikin wadannan zane-zanen jikin bango su kan ba mutane mamaki sosai.
Masanin nazarin kayayyakin tarihi na cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin Mr. Wu Xinhua ya mayar da wadannan zane-zanen jikin bango a matsayin 'laburare da ake bude a jikin bango', domin sun bayar da bayanai masu daraja wajen nazarin halin da kasar Sin ke ciki a fannin zaman al'ummar kasa na da. Ya ce, (murya ta 5, Wu Xinhua)
'Alal misali, an soma yin amfani da sulke a jikunan dawakin yaki a kasashen Turai bayan shekarar 1640. Amma a nan Dunhuang, an yi zane-zane a kan bango bisa halin da ake cikin a wannan fanni, sa'an nan kuma siffofin dawaki masu sulke da ke cikin zane-zanen jikin bango sun fito ne da wuri, in an kwatanta su da na kasashen Turai. Ban da wannan kuma, wadannan zane-zanen jikin bango sun shafi zaman rayuwar mutane. Ga misali, yanzu kowa ya sani goge hakora don kiwon lafiyar baki. An yi zane-zane a jikin bango don bayyana irin wannan hali, a cikin wasu zane-zane, ka iya ganin cewa, mutane sun tabo wasu abubuwa da yatsunsu su goge hakoransu.'(Tasallah)
|